Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Wasu daga cikin kyawawan hotuna daga ko'ina cikin nahiyar Afirka da kuma na 'yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

A picture taken on August 19, 2017 shows a woman wearing a decorative attire during the annual Chale Wote Street Art Festival at James town in Accra. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A babban birnin kasar Ghana kenan, inda wata mace ta caba ado a kan titin Chale Wote gabanin fara bukukuwan al'ada
hoton da aka dauka ranar 19, ga watan Agusta 2017 a bikin gargajiya da aka gudanar a birnin Accra. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan masu wasan kwaikwayo na cikin gida da na kasashen waje ke nishadantar da dandazon 'yan kallon da suka halarci bukuwan da aka gudanar ranar Asabar da wasanni daban-daban
wasu mata na rungumar junansu a bikin gasar dafa dukar shinkafa da aka gudanar a birnin Lagos, ranar 20 ga watan Agusta 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Haka kuma a wannan ranar ce wadannan matan ke wasa a bikin dafa-dukar shinkafa a birnin kasuwanci na Lagos da ke tarayyar Najeriya, an shirya bikin ne domin bayar da dama ga masoya da su dandana ko wacce irin dafa-dukar shinkafa a yankin yammacin Afirka, domin gano kasar da ta fi iya hada dafa-dukar.
magoya bayan jam'iyya mai mulki ta MPLA a babban birnin kasar Angola suke gangamin yakin neman zabe ranar 19 ga watan Agusta 2017. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Asabar ne kuma magoya bayan jam'iyya mai mulki ta MPLA a babban birnin kasar Angola suke gangamin yakin neman zabe. Ana sa ran dan takarar jam'iyyar ne Joao Lourenco zai zama shugaban kasar na gaba, bayan da shugaba mai ci Jose Eduardo dos Santos ya yanke shawarar sauka bayan shafe shekara 38 yana kan karagar mulki.
hotunan magoya bayan Isaias Samakuva (not pictured), dan takarar jam'iyyar UNITA rike da bakin zakara, wanda shi ne alamar jam'iyyar.a gangami na karshe na yakin neman zaben kasar a birinin Luanda na Angola Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A rana ta biyu kuma magoya bayan babbar jam'iyyar adawa da Isaias Samakuva ke yi wa takara suka gudanar da nasu gangamin rike da bakin zakara, wanda shi ne alamar jam'iyyar ta Mista Samuka.
Magoya bayan dan takarar jam'iyyar adawa na kasar Kenya Raila Odinga kenan ke zanga-zanga a birnin Nairobi ranar Juma'a., Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A nan kuma magoya bayan dan takarar jam'iyyar adawa na kasar Kenya Raila Odinga na zanga-zanga a birnin Nairobi ranar Juma'a. 'Yan adawar sun zargi 'yan sanda da amfani da karfi fiye da kima kan masu zanga-zangar bayan zaben kasar ranar 8 ga watan Agusta. 'Yan sanda dai sun karyata wannan zargin.
Gwamnonin jihohin Najeriya sun tarbi shugaban kasar Muhammadu Buhari a babban filin jirgin saman kasar da ke Abuja, ranar 19 ga watan Agusata, 2017 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Asabar da ta gabata ne wasu gwamnonin jihohin Najeriya suka tarbi shugaban kasar Muhammadu Buhari, a filin jirgin saman babban birnin tarayyar kasar Abuja, bayan dawowarsa daga jinyar da ya kwashe sama da wata uku yana yi a Birtaniya.
Ranar Asabar kenan mazauna birnin Ouagadougo babban birnin kasar Burkina Fasso ke gudanar da zanga-zanga rike da kwalaye da ke dauke da sakonnin dake cewa "ba ma son ta'addanci". Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ranar Asabar kenan inda mazauna birnin Ouagadougo babban birnin kasar Burkina Fasso ke gudanar da zanga-zanga rike da kwalaye da ke dauke da sakonnin da ke cewa "ba ma son ta'addanci". Bayan da aka yi zargin cewar 'yan ta'adda ne suka kaddamar da hari kan sanannen gidan abinci na Turkish Restaurant da ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutum 18 ranar 13 ga watan Agusta.
An dauki wannan hoton ne ranar 15, ga watan Agusta 2017, a kusa da kan iyakar kasar Chadi da Kamaru. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wannan hoton kuma da aka dauka rana Juma'ar da ta gabata, yara ne ke wasa a kogin Chari da ke N'Djamena babban birnin kasar chadi
A ranar Juma'ar ta gabata kenan wasu iyaye a birnin Alqahirar kasar Masar ke koya wa jaririnsu ninkaya a ruwa a wata makaranta irinta ta farko a kasar, ranar 15, ga watanm Agusta 2017. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Juma'ar ta gabata kenan wasu iyaye a birnin Alqahirar kasar Masar ke koya wa jaririnsu ninkaya a ruwa

Hotuna daga AFP da EPA da Getty Images da kuma Reuters

Labarai masu alaka