Kalli hotunan ziyarar ‘yan PDP ga Buhari

Wasu shugabannin jam'iyyar adawa ta PDP da na jam'iyya mai mulki ta APC sun ziyarci Shugaba Buhari na Najeriya don yi masa barka da dawowa.

Bayanan hoto,

Tawagogin jam'iyyar APC da na PDP sun kai ziyarar ne a lokaci daya da misalin karfe 11 na safe, inda Ahmed Makarfi shugaban jam'iyyar PDP ya jagoranci tawagarsa, John Odigie-Oyegun na jam'iyyar APC kuma ya jagoranci tasa tawagar

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya nuna "matukar godiyarsa da suka samu lokaci duk da irin ayyukan da ke gabansu," suka je yi masa maraba da dawowa daga jinya.

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya bukaci dukkan bangarorin da su mika sakon godiyarsa ga jama'arsu a fadin Najeriya kan addu'o'in da suka yi masa na samun sauki

Bayanan hoto,

Shugaban ya ce ziyarar ta nuna cewa Najeriya kasa daya ce mai hadin kai

Bayanan hoto,

Shugaban jam'iyyar PDP Ahmed Makarfi ya ce a shirye suke su yi "adawa mai ma'ana"