An samu manoma da laifin kisan bakar fata a Afirka ta Kudu

Reuters

Asalin hoton, Reuters

An samu wasu manoma jar fata 'yan Afirka ta Kudu guda biyu da laifin yunkurin hallaka wani bakar fata, bayan saka shi cikin akwatin gawa da kuma yi masa barazanar kona shi da rai.

Mai shari'a Sheilan Mphakele, ta ce ta bayyana karara mutanen Willem Oosthuize da Theo Jackson na shirin hallaka mista Victor Mlotshwa wanda duka aka kawo so kotun.

Wakiliyar BBC ta ce a dakin kotun da magoya bayan bakar fatar da manyan 'yan siyasa daga jam'iyyu da dama, mai shari'a Shilan Mphakele ta ce ta gamsu da yadda aka yanke hukuncin fiye da yadda wasu sukai zato.

An kama manoman biyu, bayan wallafa hoton bidiyon yadda suka yi wa mista Victor, a shafukan sada zumunta.

A nasu bangaren a kokarin kare kan su, sun ce wai suna "son koyawa bakar fatar hankali ne, saboda katsalandan din da ya yi musu na shiga gonarsu, amma ba su yi nufin su hallakashi ba."