An harbi wani mahari a Brussels

Wani mutum ne ya kai wa wani jami'in tsaro hari da wuka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mutum ne ya kai wa wani jami'in tsaro hari da wuka

An harbe wani mutum a tsakiyar birnin Brussels a kasar Belgium bayan ya nemi ya daba wa sojoji biyu wuka, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Hotuna daga wajen sun nuna cewa 'yan sanda sun kebe wurin da al'amarin ya faru da shingaye.

Wani ganau Ryan MacDonald, ya ce ji kara harbin.

Babu tabbacin ko maharin ya tsira ko kuma a'a. Rundunar 'yan sandan birnin ba ta yi wani karin haske ba game da lamarain ba.

Za mu ci gaba da kawo muku karin bayani...

Labarai masu alaka