Niger: Manoma da makiyaya na samun horo kan zaman lafiya

An jima ana samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An jima ana samun rashin jituwa tsakanin manoma da makiyaya

Rikici tsakanin manoma da makiyaya abu ne mai tsohon tarihi a Jumhuriyar Niger.

Tun shekaru da dama da suka gabata, tashin hankali tsakanin bangarorin biyu ya kasance tamkar ruwan dare a yankunan karkara.

Lamarin fada tsakanin manoma da makiyaya yafi gudana ne a a lokacin damuna.

A mafi yawan lokuta barnar da ake cewa dabbobin makiyaya na yi a gonakin manoma da mayar da wurin kiwo gona da dai sauran su, na daga cikin ire-iren abubuwan da ke haddasa rikicin.

Image caption Manomi a Niger

Shi dai irin wannan rikici da zarar ya wakana sai an samu asarar rayuka da dukiya.

Ganin irin dumbin asarar rayuka da dukiya da ake samu sanadiyar irin wannan rikice-rikice na jahilci a kasar ta Niger, yanzu haka a jihar Damagaram da ke gabas masu kudanci da kuma ta kasance wani yankin da al'ummomin biyu ke zaune a tsakanin su , na bayar da horo ga bangarorin biyu ta yadda za su zauna da juna lafiya.

Image caption Kiwo tushen arziki

Wata kungiya ce mai suna FENAP ta shirya wannan bayar da horon da nufin taimaka wa bangarorin fahimtar juna, abun da ya gagara shekara da shekaru a tsakaninsu.

Noma da kiwo sun kasance manya-manyan hanyoyin samar da arziki a kasar ta jumhuriyar Niger.

Labarai masu alaka