Congo: Mutane milyan 4 sun tserewa rikici

Shugaban kasar Congo, Joseph Kabila Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban kasar Congo, Joseph Kabila

Tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci sun sa mutane milyan 4 baro yankin kudanci Kasai na kasar Congo.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, ta sanar da cewa a yankin na kudancin Kasai, rade-radi na cewa ana kashe mutane tare da yi wa mata fyade.

Tun dai bayan kisan wani basarake na wata kabila da ke kudancin Kasai ,sojan sa kai 'yan kabilar suka dauki makamai,Kuma su ke ta arangama da dakarun gwamnatin kasar a wani mataki na mayar da martani kan kisan basaraken dan kabilar su.

Yanayin da masu baro yankunan na su ke ciki bashi da dadin fadi kamar yadda wasu kafofin dillancin labarai suka ruwaito.

Kasar Congo dai ta kasance wani dandalin yake-yake da tashe -tashen hankula da suka ka ki karewa tsawon shekara da shekaru.

Labarai masu alaka