Da alamu raguna za su yi kwantai a Nigeria

Ba bu cinikin raguna a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba bu cinikin raguna a Najeriya

A dai-dai lokacin da ya rage kasa da kwana bakwai a gudanar da bukukuwan babbar sallah, a Najeriya raguna na nan jibge a kasuwanni babu masu saya .

A wannan shekarar, da dama daga cikin masu sayen Raguna da wuri-wuri kamar yadda aka saba a baya, ba su halarci kasuwa ba har zuwa yanzu.

Masu sayar da dabbobi a kusuwanni sun ce, duk da kudaden ragunan sun banbanta da na bara, ba a zuwa ana saya sosai.

Masu sayen ragunan da yanzu suka siya, sun shaidawa BBC cewa, farashin ragunan a bana da sauki idan aka kwatanta da na bara.

A bara dai sai da aka kai raguna sayarwa a kasuwanin Jamhuriyar Nijar daga Najeriya sanadiyar tabbarbarewar darajar da kudin kasar wato Naira ya yi.

Tambayar ita ce, shin ko a bana ma saboda rashin cinikin raguna yayin da Sallah ke karatowa zai sa 'yan kasuwa fita da ragunan nasu zuwa kasashen waje?

Labarai masu alaka