Dantata
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kun san zuri'ar da suka fi kowa kudi a Nigeria?

Alhaji Hassan Sanusi Dantata jika ne ga hamshakin attajirin nan, Alhaji Alasan Dantata, kuma ya yi wa BBC karin bayani game da tarihin marigayin lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan kwanakin baya.

Alhaji Hassan wanda shi ne ya rubuta littafin tarihin rayuwar attajirin, ya bayyana irin gwagwaryamar da ya sha a fannin kasuwanci a tsakanin shekarun 1880 zuwa 1955.

Har ila yau marubucin ya bayyana dangantakar da ke tsakanin marigayi Alasan Dantata da mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka wato Alhaji Aliko Dangote.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da abokin aikinmu, Ahmad Abba Abdullahi, ya yi da jikan dan kasuwan idan kuka latsa alamar lasifika da ke hoton sama.

Labarai masu alaka