Mun kusa murkushe 'yan Boko Haram — Kuka-Sheka

Sojojin Najeriya sun ce suna samun nasara a yakin da suke da Boko Haram Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY TWITTER
Image caption Sojojin Najeriya sun ce suna samun nasara a yakin da suke da Boko Haram

Makonni bayan da gwamnatin Najeriya ta umarci manyan hafsoshin sojin kasar su koma birnin Maiduguri da zama a ci gaba da yaki da Boko Haram, ganin yadda ake samun karuwar hare-haren kungiyar, rundunar sojin Najeriyar na cewa wannan mataki ya fara yin tasiri sosai.

Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka, shi ne kakakin rundunar mayakan kasa ta Najeriyar, ya shaidawa BBC cewa, kamar yadda ake gani rundunar tasu ta yi kokari wajen kakkabe 'yan Boko Haram, abin da ya rage kalilan ne kawai.

Ya ce yanzu sun bullo da wasu sabbin dabaru da kuma kayan aiki domin samun nasara a yakin da rundunar sojin take da 'yan Boko Haram.

Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya kuma yi karin bayani a kan inda aka kwana a umarnin da aka ba su na cewa ko su kamo Shekau ko kuma su kashe shi cikin kwana 40, inda ya ce suna nan suna kokari dai-dai gwargwadon hali.

Ya ce akwai wata rundunar da suka kebe daga cikin sojojin nasu wadanda aka basu horo na musamman da kuma makamai, kuma da taimakon rundunar sojin sama ta Najeriya ana kai farmaki duk inda ake zaton akwai 'yan ta'adda.

Birgediyan ya ci gaba da cewa, kafin cikar wa'adin da aka dibar musu, za'a samu cimma buri.

Ga dai yadda hirar tasa ta kasance da Ahmad Abba Abdullahi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Kuka-Sheka da Ahmad Abba Abdullahi

Labarai masu alaka