Bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa birnin Houston Amurka

Ambaliya a Houston Hakkin mallakar hoto Rex Features

Kamar yadda jami'ai a jihar suka nuna Houston na cikin juyayi bayan shaida wata babbar guguwa mai tafe da ruwa a cikin tarihin jihar Texas.

An shaida saukar ruwan sama mai yawan centimita 75, yayin da guguwar hurricane harvey ke ratsawa ta koguna - al'amarin da ya janyo ambaliyar ruwa a kan hanyoyi ya mayar da titunan birnin kamar koguna.

Ana dai hasashen cewa cikin wannan makon a bana yankin zai shaida saukar ruwan sama mai yawa. An rawaito cewa mutum biyar sun hadu da ajalinsu a yayin da kuma jirage masu saukar ungulu ke ciccibo mutanen da suka makale a kan runfunan gine-ginen gidaje.

Daukin da ake kai wa mutanen dai na neman gazawa - wannan ne ya sa mutane ke ta kokari tsira da kansu.

An dai yi kiyasin guguwar hurricane za ta kai girman ma'auni na hudu . To amma daga bisani aka rage girma ma'aunin zuwa guguwa da ke keta dazuzzuka.

Kimanin mutum 2,000 ne aka ceto daga ciki da kuma kewayen Houston - birni na hudu mafi girma a Amurka. Birnin Houston dai na da yawan bil'adama kimanin miliyan shida da dubu dari shidda.

Tuni dai aka janye wani gidan kula da gajiyayyu a Dickson ta jirgi mai saukar angulu zuwa wani waje mai nisan kamar kilomita hamsin (50km) da ke a kudu maso gabashin wajen birnin.

Wannan kuwa ya biyo bayan wasu hotuna da aka warwatsa ta hanyoyin sadarwa irin na zamani a kan yadda tsoffi d ake zaune a gidan gajiyayyu ke neman a kai musu dauki.

Hukumar kula da yanayi da saukar iska ta bayyana cewa al'amarin da ya faru ya zo musu a ba zata. Ana dai ci gaba da shaida barazanar ambaliyar ruwa a wasu yankuna sa'annan har zuwa wannan lokaci akwai yankunan da kaiwa a gare su ke bai wa hukumomi wahala.

Dubban gidaje ne aka yanke musu hasken lanatarki, tun bayan afkuwar wannan al'amari. Da yawa daga makarantu na ci gaba da zama a rufe. Sa'ilin da biyu daga manyan filayen jirgin sama ambaliyar ruwa ta yi makil a cikinsu.

Birnin Houston na cikin matsala- a cewar James Cook na BBC.

A yanzu ruwan sama ya mamaye daukacin birnin -an kulle shaguna da sauran harkokin kasuwanci. An killace hanyoyin mota da a ke bi a cikin birnin. Sa'annan kuma an kulle tasoshin filin jirgin sama - akwai yiwuwar tafiye-tafiye su fuskanci matsala watakila ba masu yiwuwa ba ne.

Bayan ka iwa mutane dauki, an kuma tashi wani asibiti - dab da lokacin da injiniyoyi ke ci gaba da aiki bil hakki don a saki ruwan da ya bakam daga madatsun ruwa biyu.

Ana ci gaba da gargadin masu gidaje da ke makwabtaka a kusa da madatsar ruwa da su kwana da shirin fuskantar ambaliyar ruwa cikin wasu sa'oi masu zuwa.

Wasu daga mazauna wadannan yankuna dai na zaune cikin damara tun bayan da ruwan ya nausa zuwa yankin Gulf a Mexico a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Akwai wani yanki da ke makwabtaka da wadannan yankuna da suka fara shaida ambaliyar ruwa - wasu mutane na cike da fushi tun bayan da aka sanar da su cewa su kaurace yankunansu cikin dare daya.

Wannan dai ya zo a lokacin da ruwan ke tinkaro su da tsanani.

Hukumomi dai na ci gaba da gudanar da ayyukansu To sai dai ana duba ko ta wacce hanyar ce za su samarwa shugaban kasar Donald Trum muhalli a daidai lokacin da ayke shirin kai wata ziyara jihar Texas a Talatan nan. In har shugaba Trump y ace zai ci gaba da kai ziyara birnin to lalle idanunsa za su gane ma sa yadda birni mai arzikin mai ya zama abin tauayi

Anya ana samun saukin kawar da ambaliyar ruwan?

Za a ce babu alama. Bisa la'akari da yadda ruwan mai tafe da guguwa ke ci gaba da ragargazar kudu maso gabashin Texas. Sa'annan ruwan na ci gaba da tumbatsa kuma ke nausawa zuwa Houston.

Magajin garin Houston Sylvester Turner, ya fadawa mazauna birnin cewa, 'Kar ku yi gaggawar kusantar hanyoyi birnin. Kar ku yi tunanin cewa wannan guguwa ta zo kuma ta wuce.'

Dubban mutane ne da aka umarce su da su bar yankin Fort Bend kamar tsawon kilomita hamsin da biyar kudu maso yammacin Houston - wani yanki da ake tinanin kogunan yankin za su cika su batse.

Kawo wannan lokaci hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a game da shirin janye mutane daga yankin ba.

Kome ya sa basu bayar da sanarwar ba?

Magajin garin Turner a wannan Lahadin da ta gabata ya kare kansu daga shirin da aka yi na kwashe mutum kimanin miliyan biyu da dubu dari uku.

Ya bayar da misali da abin da ya faru a Houston a yayin da aka dauke mazauna yankin a dab da lokacin da mahaukaciyar guguwar Hurricane ta sauka a watan satumba a shekara ta 2005.

Mutane sun makale sama da sa'a 20 a kan hanyoyi ba tare da an kai musu dauki ba. Hakan ya haifar da mutuwar gomman mutane.

Ana dai hasashen cewa guguwar Rita za ta nausa zuwa Houston ta tsallaka zuwa gabashin birnin.

Masu kula da al'amura dai na bin bahasin yadda aka yi jigilar mutane ta hanyoyin da ba su dace ba kafin saukar mahaukaciyar guguwar Hurricane Katrina da ta ci yankin Nw Orleans a cikin watan Agustar da bala'in ya sauka.

Dubban mutane sun yi zaman wahala a wani yanayi da suka fuskanci karancin ruwa.

Wacce illa guguwar Harvey za ta yi ga tattalin arzikinsu?

Yankin gabar tekun Texas wani bangare ne mai muhinmanci ga harkokin man fetur da isakar gas a kasar Amurka. Dalili kuwa wasu daga manyan matatun man fetur da ke a jihar Texas sun dakatar da ayyukansu.

Wannan na haifar da damuwa bisa la'akari da cewa zai jefa al'ummar kasar cikin matsalar karancin man fettur da kuma tashin farashin man fetur.

Ana dai ci gaba da kiyasta hasarar da guguwar mai tafe da ruwan sama ta haifar.

Kwararru a kan harkokin Inshora kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, suna cewa babu mamaki wannan bala'i ya kasance wani mafi girma da Amurka ta taba shaidawa.

Idan akayi la'akari da cewa guguwar Katrina ta haifar da hasarar kimanin dala biliyan 15 da ambaliyar ta haifar a jihar Liousiana.

Labarai masu alaka