Yaushe Buhari zai soma yi wa jama'ar Kano aiki?

Yadda Kanawa suka zabi Buhari

Irin kuri'un da suka kada masa a 2015

9,401,288

Yawan al'ummar Kano

  • 2,172,447 Yawan kuri'un da aka kada a zaben 2015

  • 1,903,999 Kuri'un da Buhari ya samu

  • 215,779 Kuri'un da Jonathan ya samu

Ofishin Shugaban Najeriya

Duk wanda ya san Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kwana da sanin cewa babu wata jiha da ta ba shi goyon baya kusan dari bisa dari kamar jihar Kano.

Tun lokacin da ya tsunduma harkokin siyasa Kanawa suka dora aniyyar tallafa masa - komai ruwa, komai dari.

A duk lokacin da ya samu zarafi, shi kansa Shugaba Buhari yakan bayyana irin kaunar da Kanawa ke yi masa.

Kusan a iya cewa idan ban da sabanin da aka samu tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau, a siyasance babu wata babbar matsala da ta fito fili tsakaninsa da Kanawa.

Al'ummar Kano na kallon shugaban na Najeriya a matsayin mutumin da zai yaye musu kuncin rayuwar da suke ciki.

Shi ya sa a zaben 2015 suka jefa masa kuri'a fiye da duk wani dan takarar shugaban Najeriya - inda ya samu kusan kuri'a miliyan biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kuri'ar da Buhari ya samu a Kano ta fi ta kowacce jiha a zaben shekarar 2015

'Mun yi namu, saura nasa'

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wasu masu nazari kan harkokin siyasa dai sun ce halascin da Kanawa suke nunawa Shugaba Buhari wata alama ce da ke nuna cewa har yanzu shugaban ba shi da wata cibiya ta siyasa tamkar Kano.

A cewarsu, zaben da suka yi masa ya ba shi wata dama da zai saka musu tun da dai su sun yi bakin kokarinsu wurin nuna masa halasci.

Sai dai masana siyasa irinsu Dokta Kabiru Sai'du Sufi na Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a a Kano, sun bayyana cewa gwamnatin Buhari ba ta yi wani abin a zo a gani ga Kanawa domin nuna musu cewa ba su yi zaben tumun-dare ba.

"Ina ganin abin da ya sa Shugaba Buhari bai yi wa Kanawa aiki ba shi ne kalamin da ya yi a Chatham House da ke Ingila, inda ya ce zai ba da muhimmanci ga jihohin da suka zabe shi.

"Hakan ya jawo masa suka daga wasu bangarorin Najeriya, kuma an sanya masa ido a gani ko zai nuna bambanci, shi ya sa a ganina ya juyawa Kano baya", in ji shi.

Dokta Sufi ya kara da cewa: "Hausawa sun ce don lada ake Sallah. Idan ka duba za ka ga cewa gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi wa Kanawa komai ba yayin da take ayyuka a yankin kudu maso yammacin kasar nan.

"Ka duba titin Kano zuwa Kaduna ko titin Kano zuwa Maiduguri, kai idan na yi maka irin ta mahaukaci za a iya cewa idan ban da a makon jiya da shugaban kasa ya ba da umarnin a gina titin dogo daga Kano zuwa mahaifarsa Daura, babu abin da aka yi wa Kano.

"Ya kamata a ce titin da za a gina daga Legas zuwa Kano ya zama daga Kano zuwa Lagos", in ji mai sharhin a kan sha'anin siyasa. "

Ya kara da cewa rashin mayar da hankali a kan jihohi irinsu su Bauchi da Jigawa da Kano zai sanyaya gwiwar masu zabe a wadannan jihohi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Al'ummar Kano sun yi wa Buhari ruwan kuri'u a zaben 2015

A cewarsa, "Masu zabe za su ga cewa idan ma sun kadawa mutum kuri'a ba lallai ne ya yi musu aiki ba, don haka za su daina nuna karsashi wajen nuna soyayya ga 'yan siyasa irin su Shugaba Buhari".

Sai dai makusantan shugaban kasar sun ce Shugaba Buhari bai manta da jihar Kano ba kuma ma ya soma yi wa jihar ayyuka.

Mallam Bashir Ahmad, mai bai wa shugaban shawara a kan harkokin shafukan sada zumunta, ya shaida wa BBC cewa Shugaba Buhari ya inganta harkokin noma a jihar ta Kano.A cewarsa, "Ita gwamnatin tarayya ba kamar gwamnatin jiha take ba inda za a ce ta raba ayyuka zuwa jiha-jiha.

"Amma duk da haka Shugaba Buhari ya hada gwiwa da gwamnatin jihar Kano wajen farfado da kamfanin KASCO na takin zamani yadda aka inganta noma, kasancewar akasarin al'ummar Kano manoma ne.

Haka kuma a kasafin kudin shekarar 2017, an sanya gyara hanyar Kaduna zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maiduguri baya ga layin dogon da aka soma daga Lagos zuwa Kano."

Hadimin na shugaban Najeriya ya kara da cewa akwai bukatar Kanawa da ma sauran 'yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatinsu, yana mai cewa sannu a hankali za ta cika alkawuran da ta dauka.

Sai dai abin da masu nazari a kan harkokin siyasa ke tambaya shi ne: shin yaushe za a yi wa Kanawa wadannan ayyuka da hadimin shugaban kasa ke cewa za a yi ganin cewa yana can yana ayyuka sosai a jihohi irinsu Lagos? Kuma ma, shin wannan shi ne ladan goyon bayan da Kanawa suka yi wa Shugaba Buhari wanda har yanzu ko sau daya bai taba kai ziyara jihar ba duk da cewa ya kai ziyara a wasu jihohi wadanda basu zabe shi ba?

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'ar Kano sun yi ta bukukuwan murna da samun nasarar da Buhari ya yi