Koriya ta harba makami mai linzami ta saman Japan

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda aka tashi da bala'in giftawar makami mai linzami a Japan

Koriya Ta Arewa ta harba wani makami mai linzami ta sararin samaniyar Japan, wani al'amari da Firai Ministan Japan Shinzo Abe ya ce hakan wata babbar barazana ce da ba a taba samun irin ta ba.

An harba makamin ne a ranar Talata da sassafe agogon Koriya, wanda ya bi ta tsibirin Hokkaido kafin daga bisani ya fada cikin teku.

Ana sa ran Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani taron gaggawa don mayar da martani kan lamarin.

A baya-bayan nan ne Koriya Ta Arewa ta aiwatar da wasu gwaje-gwajen makamai masu linzami, amma wannan ne karo na farko da ta harba mummunan makami mai linzami ya bi ta samaniyar Japan.

A karo biyu a baya da rokokinta suka bi ta samaniyar Japan a shekarar 1998 da ta 2009, Koriya Ta Arewa ta ce tana kaddamar da tauraron dan adam ne ba makamai ba ne.

Wakilin BBC a Tokyo Rupert Wingfield-Hayes, ya ce ga alama wannan makami na farko da aka harba wanda ka iya daukar makamin nukiliya.

An umarci mazauna kasar su nemi mafaka

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
N Korea's Japan missile: The key questions

Rundunar sojin Koriya Ta Kudu ta ce an harba makami mai linzamin ne ta gabas kafin karfe 6:00 na safe, wanda ya yi daidai da karfe 9:00 na daren Litinin agogon GMT, daga Pyongyang, babban birnin kasar, wanda ba a cika samun hakan ba.

Wani sharhi da aka yi na farko ya nuna yadda harbin makamin ya kasance:

  • ya yi tafiyar fiye da kilomita 2,700
  • ya yi kama da samfurin Hwasong-12, wani sabon samfurin makami da ba a dade da kera irinsa ba
  • nisansa daga kasa ya kai kilomita 550, wanda hakan shi ne gwajin da ya fi yin kasa-kasa a duk gwaje-gwajen makamin da Koriya ta yi a baya-bayan nan
  • ya fada tekun Arewacin Pacific kilomita 1,180 kusa da gabar tekun Japan, bayan ya ragargaje zuwa gida uku

Japan dai ba ta yi wani kokarin harbo makamin ba amma ta fitar da sanarwar gargadi ga 'yan kasar da ke Hokkaido da su nemi mafaka a gine-ginen da suke karkashin kasa.

Kwanan nan ne dakarun Amurka da na Japan suka kammala wani atisaye na hadin gwiwa a Hokkaido yayin da ake ci gaba da wani atisayen na dubun-dubatar dakarun Koriya Ta Kudu da Amurka a Koriya Ta Kudun.

Koriya Ta Arewa na kallon wannan atisaye na hadin gwiwa da ya hada da sojojin Amurka a matsayin wata tsokana, inda suke ganinsa a wani yunkuri na kai mata hari.

Shugaban kasar Koriya Ta Kudu Moon Jae-in, ya bayar da umarnin dakarun kasar su fito su yi gagarumin atisaye don mayar da martani ga harin. Jiragen yakin Koriya Ta Kudu sun yi ta atisayen harba bama-bamai a ranar Talata.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Firai Minsitan Japan Shinzo Abe ya yi mummunar suka ga harin

Mr Abe ya ce ya yi magana da Shugaba Donald Trump kuma duk su biyun sun amince a kara matsa wa Koriyta Ta Arewa lamba.

Sai dai cibiyar tsaro ta Amurka ta ce wannan hari ba barazana ce ga kasar ba, amma sojoji na aiki don tattara bayanan sirri game da harin.

China ta yi gargadi cewa tashin hankali ya kai kololuwa a yankin Koriya, amma ta ce Amurka da Koriya Ta Kudu ne abin zargi. Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron China Hua Chunying, ta soki kasashen biyun da ci gaba da atisayen sojin da suke yi wanda ke zama kamar matsin lamba ga Koriya Ta Arewa.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov, ya ce, kasar ta damu matuka a kan yiwuwar tabarbarwar da lamarin zai yi, amma ya ce atisayen da sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu ke yi yana kara harzuka Koriya Ta Arewa.

Sharhi: Rupert Wingfield-Hayes, na BBC a Tokyo

Ana ganin wannan ne gwajin makami mai linzami mafi muni da Koriya Ta Arewa ta yi a lokaci mai tsawo. Kwarai jiragen Koriya Ta Arewa na bi ta sararin samaniyar Japan a da, amma wannan ne karo na farko da Pyongyang ta harba makamin nukiliya ta saman Japan.

Sharhin farko da aka yi ya nuna cewa makamin samfurin Hwasong-12, wanda aka fara ganinsa a wani babban faretin soji a Koriya Ta Arewa a watan Afrilu. Daga bisani kuma aka fara harba shi cikin teku a watan Mayu.

Me ya sa Koriya Ta Arewa ta zabi yin hakan a yanzu? Na farko dai tana son nuna jajircewarta. Tana nuna cewa barazanar Amurka ba ta bai wa kasar tsoro, kamar yadda Shugaba Trunp ya fada mako biyu da suka gabata.

Na biyu, Koriya na son sake gwada makamin nata a gwaji na hakika. Na uku irin wannan gwaji na zama matsin lamba ga kawancen Amurka da Koriya. Yana sa Japan na jin rauni sosai yayin da yake kalubalantar jajircewar Amurka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An yi ta tura wa mutane sakon kar-ta-kwana a Hokkaido ana gaya musu su nemi mafaka

Labarai masu alaka

Karin bayani