Hotunan muhimman wuraren ziyara a Makka da Madinah

Wadansu hotunan wasu muhimman wurare ne da ake ziyarta a lokacin da mutum ya je aikin Hajji ko Umarah ciki har da hoton masalalci mai Alkibla biyu. Abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya dauko mana wasu daga cikinsu.

Masaallacin Qiblatain
Bayanan hoto,

Wannan wani masallaci ne mai dimbin tarihi a addinin Musulunci. A wannan masallaci ne lokacin da Manzon Allah (SAW) ke jan al'ummar Musulmai sallah aka yi masa wahayi da cewa ya juya daga kallon Masallacin Kudus zuwa kallon Ka'aba. Inda take Manzon Allah ya bi wannan umarni ya juya kuma mamu suka bi sahunsa. Shi ne ake kiran masallacin da Masjid Kiblatain, wato masallaci mai alkibla biyu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Makabartar Baki'a ke nan a Madinah, inda nan ne aka binne mafi yawan sahabban Manzon Allah (SAW ) da wasu daga cikin ahalinsa

Bayanan hoto,

Alhazai da masu Umarah ko yawon bude ido kan ziyarci wannan makabarta ta Baki'a mai dumbin tarihi a Musulunci

Bayanan hoto,

Dutsen Uhud na arewa da birnin Madinah ne. A can ne aka yi yakin Uhud tsakanin Musulmai da kafiran Makkah, inda Sahabbai 70 suka yi shahada. Ana so mahajjata ko masu aikin Umara su kai ziyara wajen

Bayanan hoto,

Wannan shi ne wajen da aka binne Sahabbann da suka yi shahada a yakin Uhud. Kaburburansu ne nan a kusa da Dutsen Uhudun

Bayanan hoto,

Mahajjata kan tsaya gaban kaburburan su yi wa Sahabbai sallama da addu'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masallacin Kuba shi ne mafi dadewa a tarihin Musulunci baya ga Ka'aba da Kudus. Shi ne masallacin da Annabi Muhammad (SAW) ya dasa harsashin gina shi kafin masallacin Madina. A nan ne ya fara yin sallah bayan hijirarsa daga Makka kafin ya karasa cikin Madinah

Bayanan hoto,

Ana so duk wanda ya kai ziyara masallacin Kuba ya yi alwala ya yi sallah raka'a biyu

Bayanan hoto,

Gonar dabinai, wata gona ce da Manzon Allah (SAW) ya dasa a wata unguwa da ake kira Awali, tana wajen birnin Madina. Ita ma mahajjata kan ziyarci wajen idan suna da muradi