Gwamnatin Buhari 'ta kai karar mutum 6,646 kotu a shekara daya'

Shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yaki da cin hanci na cikin manyan alkawuran da Shugaba Buhari ya yi

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi karar mutum 6,646 a kotu bisa aikata laifuka daban-daban a tsakanin shekarar shari'a ta 2015-2016.

Wata sanarwa da kakakin ministan shari'a Abubakar Malami, ya aikewa manema labarai ta ce 325 cikin laifuka 1,330 kanane.

Kakakin, Comrade Salihu Othman Isah, ya ce an yanke hukuncin da ya goyi bayan gwamnati kan kashi 90 cikin dari na karar da ta shigar.

Ya kara da cewa gwamnati ta yi tsimin sama da N119 bn da kuma $14bn a cikin wadannan kararraki.

Kazalika, a cewar sanarwar, gwamnati ta hana masu laifi guje wa biyan harajin da ya wuce N10bn wanda ya kamata su biya hukumar kwastam.

"Wadannan kararraki sun hada da na manyan laifukan, ta'addanci, satar mai, kisan kai, fyade, fashi da makami da mallakar makami ba bisa ka'ida ba dai dai sauransu", in ji sanarwar.

Gwamnatin Shugaba Buhari, wacce ta dare kan mulki a shekarar 2015, ta sha alwashin yaki da cin hanci da ta'addanci da makamantansu.

Sai dai masu sharhi na ganin har yanzu gwamnati ba ta daure manyan jami'an da ake zargi da wawure kudin kasar ba.

Labarai masu alaka