EFCC na shirin taso keyar Diezani Allison-Madueke

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku saurari hirarmu da Ibrahim Magu

Shugaban riko na hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ya ce nan ba da dadewa za su sa gwamnatin Birtaniya ta tiso keyar tsohuwar ministar mai Diezani Allison Madueke.

Ibrahim Magu ya shaida wa BBC cewa "Muna nan muna kokarin ganin an taso keyarta domin ta zo nan".

Ya kara da cewa a wannan shekarar kadai, EFCC ta yi nasarar kwato kimanin Naira Biliyan 409 da kuma Dala Miliyan 69 daga hannun mutane daban-daban da ake zargi da sace kudaden gwamnatin a wannan shekarar.

A cewarsa, an gurfanar da mutanen a gaban kuliya, yana mai cewa EFCC ta samu nasara kan kararraki 137 a shekarar 2017.

Mr Magu ya ce babu wata rashin jituwa tsakaninsa da ministan shari'ar Abubakar Malami, yana mai cewa "wannan labarin sharrin 'yan jarida ne kawai. Amma buri daya muke son cimmawa".

Shugaban na EFCC ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da ba shi hadin kai a yakin da hukumar ke yi da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati.

Labarai masu alaka