Hajj 2017: Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau

Arafat, Saudi Arabia

Asalin hoton, Getty Images

Maniyyata fiye da miliyan biyu ne ake sa ran za su fara zaman Mina daga ranar Larabar nan, a wani bangare na ibadar aikin hajjin bana tsawon kwana biyar a kasar Saudiyya.

Dubban daruruwan maniyyata musulmi na ta isa Saudiyya daga sassa daban-daban na duniya domin aikin hajjin, ciki har da maniyyatan kasar Iran, bayan sun kauracewa aikin bara saboda turereniyar shekarar 2015 da ta yi sanadin mutuwar maniyyata kimanin 2,000.

Maniyyata na fuskantar kalubalen sauke farali, inda Saudiyya kuma ke fuskantar kalubalen samar da yanayi mafi kyau da ingantaccen tsaro ga maniyyatan.

Abin alfahari

A bana kawai, kasar ta tanadi dakaru fiye da dubu 100 domin tabbatar da tsaro da doka da oda a wuraren da ake gudanar da ayyukan ibada.

Dakaru sun yi atisaye na musammam domin tabbatar da shirin ko-ta-kwana da kuma tunkarar barazanar da ka iya tasowa.

Back flip

Asalin hoton, Reuters

Shekaru biyu da suka gabata fiye da maniyyata dubu biyu sun rasu sakamakon turereniya. Kasar Iran ta rasa wasu daga cikin 'yan kasarta, dalilin da ya sa ta dora wa Saudiyya alhakin lamarin.

A bara Iran ta hana maniyyatan kasarta zuwa aikin hajji, amma a bana sun je. A wani bangaren kuma akwai batun siyasar yankin -- inda rikicin Saudiyya da Qatar ya shafi maniyyata daga kasar, wadanda a da har sun fitar da rai ga halartar aikin hajjin a bana.

Ban da wannan kuma akwai batun kiwon lafiya.

Shugaban kungiyar Red Crescent a Saudiyya ya ce sun kammala shirye-shirye tare da ma'aikatar lafiya domin tunkarar barkewar cutuka ko annoba a lokacin wannan aikin hajjin.

Soldier

Asalin hoton, Reuters