Nigeria: Evans ya amsa lafinsa na 'satar mutane' a kotu

Evans lauya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya Evans ya yi karar rundunar 'yan sandan Najeriya bisa zargin suna tsare shi ba bisa ka'ida ba

Madugun nan da ake zargi da satar mutane don karbar kudin fansa a Najeriya, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na hada tuggu don sace mutane ya yi garkuwa da su a gaban wata babbar kotu a Legas.

An gurfanar da Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ne a ranar Laraba a babbar kotun jihar da ke Ikeja a gaban mai shari'a Akin Oshodi.

Tun a farkon watan Yuni ne aka cafke Evans da wasu mutum biyar inda daga bisani aka gurfanar da su a gaban babbar kotun kan tuhumarsu da satar mutane don karbar kudin fansa.

A ranar Talata ne wani sashe na babbar kotun ya sanya ranar 5 ga watan Satumba don sauraron uzurin lauyan Evans da lauyoyin 'yan sanda a kan dalilin da ya sa kotu ba za ta yanke hukunci kan karar da Evans ya shigar kan tauye 'masa hakki' na ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi gaban shari'a ba.

A ranar Talata ne kuma, wadda tun farko alkali ya so yanke hukunci kan korafin Evans din, lauyan 'yan sanda David Igbodo, ya shaida wa manema labarai cewa, "Yin hakan rashin adalci ne ba tare da jin nasu uzurin ba."

Image caption 'Yan sanda na cikin shirin ko-ta-kwana don raka Evans gidan yari
Hakkin mallakar hoto AFP

Ya kuma kara da cewa, binciken da 'yan sanda suke yi kan Evans din ya kusa kammala.

Mr Igbodo ya kuma ce binciken da suke yi din ne dalilin da ya sa suke ci gaba da tsare shi ba tare da gurfanar da shi a gaban shari'a ba, kuma kotu ce ta ba su wannan umarnin.

"Nan ba da dadewa ba 'yan Najeriya za su san mece ce makomar Evans kan irin abin da ya aikata," in ji Mist Igbodo.

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.

Tun a shekarar 2013 ne dai aka yi yekuwar neman Evans ruwa a jallo.

Labarai masu alaka