Hotunan muhimman wuraren da ake gudanar da aikin Hajji

Ga wasu hotuna da BBC ta tattaro muku na muhimman wuraren da ake aiwatar da ibadar aikin Hajji a Saudiyya.

Dutsen Hajrul Aswad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan shi ne dutesn Hajrul Aswad da ke jikin Ka'aba wanda ake so duk Musulmi ya sumbace shi da zarar ya shiga harabar masallacin gabanin ya fara dawafi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan ne wajen da ake kira Makama Ibrahim, wato nan ne inda ake so mahajjaci ya sallaci raka'a biyu. Akwai alamar sawun Annabi Ibrahim a cikin, lokacin da ya tsaya yayin da ake gina Ka'aba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan shi ne wajen Safa da Marwah inda ake so alhazai su yi sassarfa sau biyu daga Safa zuwa Marwa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Muna nan ne ainihin wajen da alhazai ke tafiya a ranar 8 ga watan Zul Hijjah don gudanar da aikin Hajji inda su kan shafe tsawon kwana hudu zuwa biyar. Waje mai matukar girma da aka gina tantuna don zaman alhazai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Filin arafah shi ne kololuwar wajen gabatar da ibadah a lokacin aikin Hajji. Wannan shi ne ainihin dutsen arafah amma ba a yanzu an fadada wajen ta yadda 'yan wasu kasashen ma su kan zauna ne nesa sosai da dutsen saboda irin cikowar da ake yi.

Asalin hoton, Twitter Muzdalifa

Bayanan hoto,

Daga arafah mahajjata kan wuce Muzdalifa don yada zango inda ake kwana sai washe gari da asuba a wuce wajen jifan shaidan.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wajen jifan Shaidan da aka fi sani da jamrah na daga cikin wuraren ibada masu muhimmanci lokacin aikin hajji.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A da a kan samu cunkoso sosai amma a baya-bayan nan hukumomin Saudiyya sun zage damtse wajen kara fadada wajen don gudun samun cunkoso.