Yadda aka kama masu cin naman mutane a Afirka Ta Kudu

Inside traditional healer's house
Image caption Police found several human body parts during a raid in a traditional healer's house

An tsinci gawar wata matashiya da ta fara rubewa mako guda bayan da wani mai maganin gargajiya ya mika kansa ga 'yan sanda ya ce ya gaji da cin naman dan adam.

Mutanen yankin KwaZulu na cike da fargaba bayan da aka gano gawar Zanele Hlatshwayo mai shekara 25, an ciccire wasu sassan jikinta, a kuayen Shayamoya a Afirka Ta Kudu.

Iyayen yarinyar wacce ta bata tun a watan Yuli, sun yi amannar cewa tana daga cikin wadanda masu cin naman mutane ne suka kashe, inda tuni aka kama biyar daga cikinsu.

Da farko dai 'yan sanda sun ki saurarar batun mutumin da ya mika musu kan nasa, amma sai suka yarda da abin da yake fada a lokacin da suka ga jini dumu-dumu a hannayensa da kafafuwansa, suka kuma kama shi.

Mutumin ya kai 'yan sandan gidansa, inda aka samu kunnen mutum har takwas a cikin tukunya.

An yi amannar cewa ya yi niyyar sayarwa abokan huldarsa ne, wadanda aka shaida wa cewar suna da sirri na taimakawa mutum ya yi kudi ko ya samu mulki.

An kuma samu wasu sassan jikin da dama a wani akwati.

Image caption An tsinci gawar Zanele Hlatshwayo a cikin duwatsu

An samu tufafin Ms Hlatshwayo da jini kaca-kaca a jiki a dakin mai maganin gargajiyar da aka samu sassan jikin mutanen.

Iyayenta ne suka gane tufafin nata.

Haka kuma, 'yan sansa na jiran sakamakon gwaje-gwajen kwayoyin halitta domin a tabbatar ko daga cikin sassan jikin mutanen akwai na wata mata mahaifiyar wani yaro dan shekara biyu.

Har yanzu iyayen Ms Hlatshwayo ba su binne ta ba. A yayin da na shiga gidansu Hlatshwayo, ba abin da nake ji sai koke-koken 'yan uwanta.

Babbar yayarta Nozipho Ntelele, ta ce min a lokacin da take share hawaye, "Muna jin ciwon salon da aka bi aka kasheta, an mata kisan wulakanci."

Image caption 'Yan uwan Hlatshwayo suna zaman makoki

Ta kara da cewa, "Duk tufafinta ya yi duku-duku da dattin kasa, alamar ta sha artabu wajen ganin ta ceci ranta," "in ji Ms Ntelele.

Warin rubabben naman mutum

Mai maganin gargajiyar na zaune ne a wata bukka a Rensburgdrift kusa da Estcourt.

Ana kiransa da "Mkhonyovu" wanda ma'anarsa ke nufin "mai tafka almundahana" a yaren Zulu na kasar.

Ya karbi hayar gidan ne daga wajen Philani Magubane, wanda shi ma ake zargin kaninsa da irin wancan laifin.

Image caption Wannan ne dakin da mai maganin ya kama haya
Image caption 'Yan sanda sun samu kunne takwas a dakin mutumin da kayan tsafi

"Na kadu matuka da jin cewa kanina ya yarda da tatsuniyar mai maganin gargajiyar nan, inda ya yi musu alkawarin arziki bayan kuwa shi talaka ne futuk," in ji Mr Magubane.

Ya ce daya daga cikin masu zaman haya a gidan ya yi ta korafin cewa yana jin warin rubabben nama na fitowa daga gidan makwabcinsa.

"Mkhonyovu bai fi wata biyu da tarewa a gidan ba, ban taba sanin cewa yana ajiye sassan jikin mutane ba saboda ni ba anan nake zama ba," in ji Mr Magubane.

Mr Magubane ya ce ya tabbata kaninsa da sauran mutanen sun rudu ne da karairayin mai maganin da ya ce zai musu tsafi su yi arziki.

Ana zargin cewa yana aika mutane su tone kaburburan jama'a ne da tsakar dare don ya hada wani tsafi da ake kira "muti".

Yadda mutane suka ci naman mutum suna sane

Mthembeni Majola, wani dan siyasa a garin ya kira taron al'ummar yankin jim kadan bayan da daka gabatar da masu cin naman mutanen a gaban kotu.

Image caption Mthembeni Majola ya ce daya daga cikin mazauna garin ya san cewa naman mutum yake ci

"Mazauna garin da dama suna zaune cikin tsoro tun bayan fallasuwar siriin mutanen, amma Mr Majola ya ce wasu mutanen ba su yi mamaki ba.

"Wasu da dama sun tabbatar da cewa sun san abin da mai maganin ke yi har ma sun ci naman mutum suna sane," in ji shi.

"Amma abin da ya bata mana rai shi ne yadda mutanenmu suka zama sakarkaru, yawancin wadanda suke zuwa wajen mai maganin barayin shanu ne wadanda yake cewa zai ba su sa'a su dinga bacewa ko ba su maganin karfe don ko 'yan sanda sun harbe su bindiga ba za ta same su ba, in ji Mr Majola.

Phepsile Maseko, wata jagora ce a kungiyar masu magain gargajiya ta Afirka Ta Kudu, ta kuma yi Allah-wadai abin da masu cin naman mutanen ke yi.

Ta ce, "Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana'armu.

Image caption Phepsile Maseko ta ce, "Mkhonyovu mai maganin karya ne wanda yake so ya yi arziki ta tsiya shi ne ya shigo da mugun abu cikin sana'arsu

"Kashe mutane da yin tsafi da sassan jikinsu ba ya cikin tsarin maganin gargajiya, abin da ya yi ya bata mana rai saboda a yanzu dole sai mun fito mun kare aikinmu da kyau gudun bacin suna," in ji Ms Maseko.

Mutane biyar din da aka kama wadanda aka gurfanar da su a kotu ranar Litinin sun yi watsi da belinsu da aka bayar, za kuma su sake gurfana a gaban kotun a karshen watan Satumba.

Labarai masu alaka