Abin da Musulunci ya ce kan yin hoto a wurin Ibadah

Selfie Hajj Hakkin mallakar hoto AHMAD GHARABLI
Image caption Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada musamman a kasar Saudiyya

Daukar hoto a wuraren ibada abu ne da mutane suke yawan yi kuma su wallafa hotunan a shafukan sada zumunta na zamani inda abokansu za su gani su kuma yi tsokaci ko magana ko kuma yayata hoton.

Ba sabon abu ba ne mutum ya dauki hoto a masallacin idi ko na harami a Makkah ko Madina ko kuma a filin Arfa.

Bugu da kari wasu na daukar hotuna na bidiyo a lokacin dawafi ko kuma lokacin hawan Arfa kuma su wallafa a shafukan sada zumunta na zamani.

Watakila wasu na yin hakan ne domin su nuna wa duniya cewa sun samu zuwa wannan waje, yayin da wasu kuma suna son su nuna wa wadanda suke gida yadda wurin ibadar yake ne.

Irin wannan dabi'ar ta samo asali ne tun zamanin da, inda mahajjata ke dawowa gida da kallo-kallo daga aikin hajji inda yara da sauran mutane da ba su samu zuwa aikin hajji ba za su samu ganin wuraren aikin hajji ta hotunan da ke cikin kallo-kallon.

Wani ma'aikacin sashen Hausa na BBC da ya sauke farali a bana, Yusuf Yakasai, ya ce ya ga dubban mutane na ta faman daukar hotuna da wayoyinsu a lokacin aikin hajjin bana.

Wasu masana harkar sadarwa dai na ganin wannan lamari wani yayi ne da zamani ya zo da shi, kuma yawaitar wayoyin salula komai-da-ruwanka ta taimaka wajen yadawa.

Sai dai tun a shekarun baya ne wannan lamari ya fara janyo ce-ce-ku-ce cikin alumar musulmai.

Sai dai dan binciken da na yi ya gano cewa mutane da dama na daukar hoto a wurin ibada ne bisa dalilai daban-daban.

Wasu da dama da na tuntuba sun shaida min cewar suna daukar irin wadannan hotunan ne saboda tarihi.

Wani dan Najeriya, Bashir Abubakar El-Nafaty, ya shaida wa BBC cewar shi yana daukar hotuna a duk wuraren da ya je na tarihi domin ya kwadaita wa 'yan uwansa zuwa irin wadannan wurare.

Da na tambaye shi ko baya ganin riya ka iya shigowa cikin aikinsa in ya dauki hoto a wani wuri daga cikin wuraren ibada, sai ya kawo hadithin Annabi (SAW) inda ya ke cewa 'Attakawa ha huna", ma'ana tsoron Allah yana nan ( a zuciya).

Ita ma Rabi'a Ayuba da na tuntubeta sai ta ce min, "Ni ban ga aibu a daukar hoto wajen ibadah ba don ina yi, sai dai kawai ni ban faye wallafawa a shafukan sada zumunta ba, amma ina ga don wasu sun wallafa ma ba lallai ya zama laifi ba."

Sai dai akwai wadanda ke ganin daukar hoto a wuraren ibada ka iya haifar da riya.

Wani dan Najeriya, Isah Yahaya Aliyu, yana da irin wannan ra'ayin.

Ya shaida min cewar daukar hoto ma ba tare da wani uzuri ba, ba abun da ake so ba ne balle daukar hoto a wajen ibada.

Da na tambaye shi ko zai dauki hoto a wuraren ibada da ke Makkah da Madina? Sai ya ce, "In Allah Ya yarda ni ba zan dauki hoto a wuraren ba domin tsoron riya ta shiga aikina.

"Amma ba wai ina nufin duk wani mai daukar hoto a wuraren ibada yana riya ba ne."

Hakkin mallakar hoto AHMAD GHARABLI
Image caption Daukar hoto domin wallafawa a shafukan sada zumunta batu ne da mutane suka saba da shi a shafukan sada zumunta

Aisha Ibrahim ma ce min ta yi, "Ni gaba daya ma hoto bai dame ni ba balle har na je wurin ibada na tsaye ina dauke-dauken hoto, gaskiya ni ba zan iya haka ba, kuma a ganina ba tsari ba ne mai kyau, musamman ma masu wallafa a shafukan sada zumunta da muhawarar nan.

"Ban sani ba ko so suke su burge mutane shi yasa suke haka."

Riya ce?

Shin mutum zai iya fitowa kai tsaye ya ce wa irin wannan dabi'ar riya?

Wasu na tunanin cewar daukar hoto a irin wadannan wuraren ibadar son a-sani ne, wato riya ce. Amma, mene ne hukuncin irin wannan dabi'ar a Musulunci?

A shekarar 2014 Jaridar Arab News ta ambato fitaccen malamin addini, Sheikh Abdul Razzaq Al-Badr, yana gargadi kan daukar hoto a lokacin aikin hajji.

Jaridar ta kuma ambato malamin yana cewa: "A duk lokacin da Manzon Allah (SAW) ya isa mikati, sai ya ce: 'Ya Allah, ka sa aikin hajjin nan babu riya a ciki ko kuma kwartamawa."

Wannan addua'ar ana yin ta ne a mikati. Kuma bayan wannan addu'ar ana aiki ne tare da dage wa kan kin bin son zuciya.

Amman yanzu a mikati mutane da dama suna daukar hoto a matsayin abun tarihi a kuma wallafa a shafukan sada zumunta. Suna daukar hoto a dawafi da filin Arafa tare da lokacin jifan shaidan."

Ustaz Hussaini Zakariya, ya ce, "Maganar daukar hoto idan aka je Harami ko Madina ko sauran wuraren ibada a ko ina a duniya, malamai sun rabu gida biyu kan wannan batu."

"Bangare daya mai tsanani ne kwarai da gaske, shi yana ganin cewa hoton ma haramun ne a ko ina aka yi, ba sai lallai cikin Harami ba, kuma yi a cikin Haramin ma ya fi muni."

Image caption Mahajjata sukan dauki hotuna a lokacin ibada a kasar Saudiyya

"Amma akwai wadanda suke ganin cewa daukar hoto ba aikin ibada ba ne. Ba wanda zai dauki hoto ya ce ya yi sunnah ko mustahabi ko kuma ya yi farilla."

Malamin ya kara da cewa: "Don haka ba aikin ibada ba ne balle a ce in ka yi jama'a sun gani, aikinka ya baci. Don haka yana ganin cewa halal ne matukar dai mutum ba wai ya yi wannan abin don jama'a su ga cewa yana wajen wata ibada kuma burinsa ya cika ba ne."

"Ya kwadaita wa wadanda Allah bai ba su ma su roki Allah Ya kai su wannan wurin, kuma ya sanar da danginsa da abokansa cewa ga shi Allah Ya kawo shi wurin da duk Musulmi yake son ya zo."

"Ina ganin wani abu ne na nuna abin farin cikin da ya samu mutum ga 'yan uwansa da abokansa."

Saboda haka Ustaz Zakariya ya ce yana ganin wannan ba aikin addini ba ne kuma ba riya ba ce.

Ga yadda amsar Malam Haussaini Zakariya ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mene ne hukuncin daukar hoto a masallatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?

Shi kuma Dokta Abdulkadir Sulaiman na Sashen koyar da addinin Musulunci a jami'ar Abuja cewa ya yi daukar hoto kansa ba ya halatta.

Amma batun ko daukar hoto tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta zai iya janyo riya, Malam ya ce wannan wani lamari ne mai sarkakiya.

Malamin ya yi bayanai tare da kawo hadisai da ke nuna cewa yanke hukuncin riya ba hurumin dan Adam ba ne domin wannan al'amari ne da ke zuciyar dan Adam, kuma Allah (SWT) ne kawai zai iya sanin abin da yake zuciyar bawansa.

Ga yadda amsar Dokta Abdulakadir Sulaiman ta kasance kan mas'alar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Akwai riya a daukar hoto a masalatai tare da wallafa shi a shafukan sada zumunta?
Hakkin mallakar hoto MOHAMMED AL-SHAIKH
Image caption Ana daukar hoton dauki-kanka har ma a filin Arfa

Labarai masu alaka