Buhari ya tafi bikin Sallah a Daura

Gwamnatin Buhari ta gurfanar da mutane da dama a gaban kuliya Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Gwamnatin Buhari ta gurfanar da mutane da dama a gaban kuliya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina ta arewacin kasar domin yin bikin babbar Sallah.

Hotunan da fadar shugaban kasar ta wallafa a shafinta sun nuna manyan jami'an gwamnati da Sarakuna suna tarbar shugaban kasar.

Cikin wadanda suka tarbe shi har da gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da sarakunan Katsina da Daura.

A ranar 19 ga watan nan ne Shugaba Buhari ya koma Najeriya, bayan ya kwashe kwana 103 yana jinyar cutar da ba a bayyana ba a birnin London.

Hakkin mallakar hoto Nigeria presidency
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin yaki da masu cin hanci
Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption 'Yan Najeriya da dama sun yi addu'a ga Shugaba Buhari lokacin da ba shi da lafiya

Labarai masu alaka