Yadda fasto ya kare Musulmi 2000 a cocinsa

Wata motar rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani limanin cocin katolika a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ya bai wa wadansu Musulmi su 2000 mafaka lokacin da suke cikin fargabar fuskantar hari daga kungiyar gwagwarmayar Kristoci ta anti-Balaka.

Fasto Juan José Aguirre Munoz ya ce Musulmin 'yan gudun hijiran ba za su bar harabar cocinsa ba a birnin Bangassou da ke kudu-maso-gabashin kasar, sai bayan ya samu tabbaci kan tsaron rayukansu.

Ya ce Musulmin da ya ba mafaka suna "fuskantar barazanar kisa" ne daga wurin mambobin kungiyar anti-Balaka.

Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Stephen O'Brien ya yi gargadin cewa akwai alamun aikata kisan kare dangi a makon jiya.

Ya ce rikicin kasar yana kara ta'azzara kuma al'amarin yana kara muni.

"Tashin hankalin yana karuwa, ana tsoron kada a kara maimaita mummunan rikicin da ya faru a kasar kimanin shekara hudu da suka wuce," in ji shi.

Mista O'Brien ya kara da cewa: "Akwai alamomin da ke nuna yiwuwar faruwar kisan kiyashi don haka wajibi ne a dauki mataki."

Labarai masu alaka