Hotunan yadda mahajjata suka jefi 'shedan' a Mina
Kimanin mahajjata miliyan biyu suke gudanar da jifan shedan a ci gaba da aikin hajjin bana a Mina kusa da birnin Makkah na kasar Saudiyya.

Asalin hoton, Getty Images
Wadansu mahajjata yayin da suka kama hanyar isa Jamarat wato wurin da ake jifan shedan
Asalin hoton, Getty Images
Wani bangare na wurin da ake jifan shedan
Asalin hoton, Getty Images
Wani mahajjaci dattijo yana kallon wurin da ake jifan shadan
Asalin hoton, Getty Images
Wata mahajjaciya tana kokarin isa wurin
Asalin hoton, Getty Images
Wani alhaji lokacin da yake kokarin yin jifa
Asalin hoton, Getty Images
Hanyoyi daban-daban da mahajjata suke isa wurin jifan daga bangarori daban-daban a Mina
Asalin hoton, Getty Images
Wani alhaji yayin da ake masa aski bayan ya yi hadaya