Hotunan abin da ya faru a Afirka makon jiya

Fitattun hotunan wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya.

People colourfully dressed at a festival

Asalin hoton, EPA

Wani bikin al'adar kabilar Ebrie wadanda suke danganta kansu da Daular Ashanti a birnin Abidjan na kasar Kwaddibuwa.

Asalin hoton, EPA

Kimanin shekara 300 ke nan ana gudanar da wannnan bikin.

Asalin hoton, Reuters

Wata 'yar kasuwa a wata kasuwar Tufafi da ke birnin Alkhahira a kasar Masar ranar Alhamis.

Asalin hoton, EPA

Wani mai sayar da dabbobi a wata kasuwar dabbobi gabanin bukukuwan babbar sallah a birnin Giza na kasar Masar.

Asalin hoton, Reuters

Wani dan bola jari a wani babban wurin zubar da shara a birnin Nairobi na kasar Kenya gabanin haramta amfani da leda a kasar cikin makon jiya.

Asalin hoton, AFP

Wani mai tallan kayan kawa yayin da ake daukarsa hoto a birnin Legas na Najeriya.

Asalin hoton, AFP

Masu tallan kayan kawan ana daukarsu hoto ne sanye da guntun siket don a wallafa a wata mujalla mai suna, A Nasty Boy Magazine, wadda fafutikar kawo daidaito tsakanin 'yan mata da maza a fannin tallata jiki.

Asalin hoton, Reuters

Wani dan tawaye a garin Yondu kusa da birnin Kaya na kasar Sudan ta Kudu.

Asalin hoton, Reuters

'Yan tawayen suna shirin kai wa wani sansanin dakarun gwamnatin Sudan ta Kudu hari ne a birnin Kaya kusa da iyakar kasar da Uganda.

Asalin hoton, Reuters

Wata 'yar ci-rani tana bai wa 'yar uwarta hakuri saboda ita ba ta samu kubuta daga wata cibiyar tsare su a birnin Tripoli na kasar Libya ba, a ranar Talata.

Asalin hoton, AFP

Wadansu masu goyon bayan wani mai fafutika, Kemi Seba, yayin da suke murnar sakinsa a birnin Dakar na Senegal ranar Talata.

Asalin hoton, Reuters

Wadansu 'yan kasar Libya lokacin da suke wasan tseren dawakai a babban birnin kasar Tripoli ranar Asabar din makon jiya.

Hotuna daga AFP, EPA, Getty Images da kuma Reuters