An zargi shugabar Burma da yin gum a kan Rohingya

Rohingyas

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hukumomin ba da agaji sun ce mutanen da ke tserewa suna cikin bukatar abinci da ruwa da kuma matsugunni

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres ya yi kira a kawo karshen abin da ya kira tarzomar keta da ke sanya dubban 'yan kabilar Rohingya tserewa.

Antonio Guterres ya ce kamata ya yi Myanmar ta ba su wani tartibin matsayi a hukumance. Ta yadda za su zama 'yan kasa ko kuma akalla su samu 'yancin walwala.

Ya ce bai kamata a ci gaba da jan kafa wajen bijiro da wani kwakkwaran shiri don magance tushen wannan rikici ba.

A cewarsa, yana da muhimmanci a ba wa musulman jihar Rakhine ko dai matsayin 'yan kasa ko kuma akalla wani matsayin shari'ah yanzu wanda zai ba su damar yin rayuwa kamar kowa.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce kimanin kashi tamanin cikin 100 na 'yan Rohingya da kwanan nan suka tsere zuwa kasar Bangladesh, mata ne da kananan yara.

A cikin wata sanarwa, asusun ya yi korafin cewa ya kasa samun damar kai wa ga kananan yara fiye da dubu 30, a ciki har da masu fama da karancin abinci da yake bai wa kulawa cikin jihar Rahkine a baya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta shaida musulman Rohingya fiye da dubu 35 da suka tsere daga kasar a cikin kwana guda.

'Yan Rohingyan sun ce suna guje wa murkushewar da sojan Burma ke yi musu ne.

Jami'ar Majalisar Dinkin Duniya ta musammam a kan kare hakkin bil adama a Myanmar, Yanghee Lee ta ce shugabar da ke rike da iko, Aung San Suu Kyi ba ta yi tir da tarzomar ba, duk da karuwar adadin mutanen da ake tursasawa arcewa.

"Ba ta ce komai ba tukunna dangane da wannan al'amari, kuma ba ta ce uffan ba kan dumbin mutanen da ke gujewa daga Myanmar, daga arewacin Rakhine.

Cikin kwana 10 da suka wuce, ina jin adadin a yanzu ya kai dubu 125."