Yadda bahaya ya kunyata budurwa a gaban saurayi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bahaya ya kunyata budurwa a gaban saurayi

Wannan rana ta zance tsakanin saurayi da budurwa ba ta kare da dadi ba. Al'amari ne da ya hada da bahaya da karya taga da kiran masu aikin ceto.

Liam Smith wani dalibi a Bristol da ke Birtaniya, ya hadu da wata budurwa a intanet, suka fita cin abinci, sai dai zance ya sauya a lokacin da suka je gidansa don huce gajiya.

A yanzu dai labarin wannan tadi nasu da bai kare ta dadi ba ya bazu tamkar wutar daji, duk da cewa dai soyayyar tana nan daram.