Me kuke son sani game da Musulman Rohingya?

Dakarun tsaron Myanmar sun ce suna yaki da mayakan sa-kai na Rohingya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dakarun tsaron Myanmar sun ce suna yaki da mayakan sa-kai na Rohingya

Majalisar dinkin duniya ta ce a kalla Musulmi 'yan kabilar Rohingya 270,000 ke neman mafaka a Bangladesh tun da dakarun gwamnatin Myanmar suka soma kashe su a mako biyu da suka wuce.

Gwamnatin Myanmar dai ta ce tana yunkuri ne na kawar da mayakan sa-kai na Rohingya wadanda ke kai mata hari, sai da wakilin BBC da ya ziyarci yankin ya ce ya ga kauyukan Musulmi wadanda aka kona kurmus.

Akasarin 'yan kasar mabiya addinin Bhudda na kallon 'yan kabilar Rohingya a matsayin bakin-haure, duk da yake an haife su a kasar.

Me kuke son sani kan wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa?

Mun daina karbar tambayoyi ta wannan shafin. Mun gode.