An yi arangama tsakanin sojoji da yaran Nnamdi Kanu

Masu fafutukar kafa Biafra Hakkin mallakar hoto Others
Image caption 'Yan kabilar Igbo da dama na ganin cewa gwamnatin Najeriya na nuna musu bambanci da wariya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta wasu rahotanni da ke cewa dakarunta sun kai hari tare da kashe mutane a garin Afaraukwu na madugun kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta karyata labarin da kungiyar ta IPOB take yadawa da ma wasu hotuna na mutane da ake cewa sojojin sun harba wadanda ake yadawa a intanet,a lokacin da sojojin suka yi wa kauyen Nnamdi Kanun dirar mikiya.

A martanin da sojojin suka yi sun ce babu wani abu makamancin haka da ya faru, illa dai wasu tsegarun kungiyar ta fafutukar kafa kasar Biafran ne suka datse hanya ga kwambar sojojin da ke kewaya birnin Umuahia na jihar Abia a ranar Lahadi da yamma, har ta kai da suna jifan sojojin da duwatsu da fasassun kwalabe.

Wannan al'amari dai ya yi sanadiyyar raunata wata mata da ke wucewa da kuma wani kofur na sojin, in ji sanarwar sojojin.

A dalilin haka ne sojoji suka yi ta harbin iska don tartatsa mutanen.

Sanarwar ta kuma ce: "Muna so mu gargadi masu ta da zaune tsaye da su daina yada karya irin wannan."

"Muna umartar mutane da su fita su yi sabgogin gabansu kamar yadda suka saba, su kuma kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba zuwa ofishin 'yan sanda."

Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun fito na fito tsakanin 'yan Biafra da jami'an tsaron kasar ba.

Ko a watan Nuwambar 2016 ma kungiyar kare hakki bil'adama ta Amnesty International ta zargi jami'an tsaron Nigeria da kisan a kalla masu zanga-zangar lumana 150 a watan Agustan 2015.

Kungiyar ta ce sojojin sun yi amfani da muggan makamai wajen murkushe masu zanga-zangar da ke neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar.

Sai dai ko a wancan lokacin rundunar sojin ta musanta zarge-zargen inda ta bayyana masu zanga-zangar a zaman barazana ga tsaron kasa.