Saudiyya ta fusata kan tattaunawarta da sarkin Qatar

An dauki wannan hoto a ranar 5 ga watan Yuli da ya wuce, hoton ya nuna wani mutum ya na wuce ofishin jirgin Qatar da ke birnin Riyadh a Saudiyya, jim kadan bayan yanke hulda tsakanin kasashen biyu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An haramtawa jirgin Qatar Airways shiga sararin samaniyar kasashen yankin Gulf da ke makoftaka da kasar

Saudiyya ta sanar da dakatar da tattaunawar da za ta kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin ta da Qatar, bayan wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin sarkin Qatar da yarima mai jiran gado na Saudiyya.

Bangarorin biyu dai sun tattauna ne kan yadda za a kawo karshen takun sakar da ke tsakaninsu wanda ya janyo Saudiyya da Bahrain, da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa yanke alaka da makwabciyar tasu.

Haka kuma, Saudiyya ta zargi Qatar da kin fadar ainihin abin da kasashen biyu suka tattauna akai, don haka a fusace ta ce ta dakatar da tattaunawar baki daya.

Tun da fari Saudiyya da kawayenta na kasashen Larabawa sun zargi Qatar da taimakawa 'yan ta'adda, zargin da Doha ta musanta.

Takaddamar da ta janyo kasashen suka hade mata kai, tare da yanke ko wacce hulda tsakaninsu tun a watan Yuni da ya wuce, ciki har da cinikayya wanda kashi 80 cikin 100 na kayan da Qatar ke amfani da su daga kasashe makwabta ake shigo da su, ciki kuwa har da kayan abinci da kayan lambu da na marmari da sauransu.

Har ila yau, hatta jiragen sama na Qatar, kasashen sun haramta musu wucewa ta sararin samaniyarsu.

Wayar tarhon da aka yi a ranar Juma'a, ta dan darsa fatan daidaituwar lamura tsakaninsu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kuma an yi wayar ne jim kadan bayan shugaba Donald Trump na Amurka ya tattauna da sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, kan batun, ya kuma nuna sha'awar shiga tsakani don kawo karshen takaddamar.

Daga bisani shugaban Amurkar ya tattauna da dukkan bangarorin biyu ta wayar tarho.

Daga nan ne kuma sarkin Qatar Tamim bin Hammad Al Thani ya kira yarima mai jiran gadon Saudiyya Muhammad bin Salman bin Abdul'azeez, suka tattauna wanda ita ce ta farko tsakanin kasashen tun bayan fara rikicin.

Kafafen yada labaran kasashen biyu sun ruwaito cewa sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad al-Thani da Yarima Mohammed bin Salman sun tattauna tare da amincewa cewar ya kamata a kawo karshen takaddamar.

Shin wa ya fara kiran wayar?

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya rawaito cewa sarkin Qatar ya nuna a shirye ya ke don a hau teburin sulhu tare da sauran kasashen hudu, sannan Saudiyya ita ce za ta yi bayanin yadda za a fara tattaunawar bayan sun cimma matsaya da kawayenta.

A bangare guda kuma kamfanin dillancin labaran Qatar ya ce Yarima Muhammad ne ya yi wa Qatar din tayin sasantawa da kuma bukatar kar hakan ta shafi manufofin kasashen biyu.

Jim kadan bayan wannan Saudiya ta fusata, tare da cewa Qatar ba ta shirya zaman tattaunawar ba da kawo karshen rikicin don haka sun dakatar da tattaunawar tsakaninsu.

Da alama dai an samu rashin fahimta ne kan yadda za a gabatar da batun, da kuma zargin da Saudiyya ta yi kan Qatar ba ta fadi ainahin yadda lamarin ya faru ba tun daga batun kiran wayar tarhon da ainahin abin da aka tattauna da kuma cimma.

Saudiyya ta zargi kamfanin dillancin labaran Qatar da cewa ya buga labarin da babu gaskiya a ciki, inda ya nuna ita ce ta bukaci Qatar din su tattauna.

Kasashen Saudiyya, da Bahrain, da Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun gabatar da wasu sharudda da suke so Qatar ta aiwatar kafin su yi sulhu da ita, ciki har da rufe kafar yada labarai ta Al-Jazeera, da janye dangataka tsakanin ta da kasar Iran.

Har ila yau kasashen na zargin Qatar na taimakawa kungiyoyin 'yan ta'adda, zargin da Doha ta musanta.

Duk wani yunkuri ko kokari na Diflomasiyya don kawo karshen rashin jituwar ya ci tura.

Shugaba Donald Trump sun tattauna ta wayar tarho da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al Thani, inda ya jaddada muhimmancin hadin kai a daidai lokacin da ake yaki da 'yan ta'adda.

Fadar White House ta ce, Shugaba Trump ya kuma bayyana muhimmancin yaki da akidun da 'yan ta'adda ke yadawa a zukatan al'umma.

Fadar ta kara da cewa yana da matukar muhimmanci dukkan kasashen su rungumi zaman lafiya da kawo karshen rashin fahimtar da ke tsakaninsu, inda ta kara da cewa rikici tsakanin manyan kasashen Larabawan abin takaici ne da zai kawo halin rashin tabbas ga 'yan kasashen da ke zaune a kasashen juna.

Dole ne dukkan kasashen su ajiye son zuciya, su sanya muradun al'ummarsu a gaba kafin wani abu. A daidai lokacin da yawancin kasashen ke fama da matsalar 'yan ta'adda na kungiyoyi irin su IS.