Myanmar: 'Ana yi wa Musulmin Rohingya kisan kare-dangi'

An dauki wannan hoto ne a ranar 5 ga watan Satumba, hoton ya nuna wani dan gudun hijira na kabilar Rohingya ya na rike da hannun wani yaro a lokacin da suke hijira ta hanyar ketara kogi cikin kwale-kwale

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kusan musulmai Rohingya 300,000 suka tsere daga kasar Myanmar tun a watan Agusta

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kare hakkin bil adama ya ce halin da musulmai 'yan kabilar Rohingya suke ciki a kasar Myanmar da kisan da ake yi musu ya yi kama da na kare-dangi.

Zeid Raad Al Hussein ya yi kira ga sojojin Myanmar su kawo karshen kisan gillar da suke yi wa musulmin Rohingya a yankin Rakhine.

Fiye da musulmai na kabilar Rohingya 300,000 ne suka tsere kasar Bangladesh tun bayan fara rikicin a watan da ya gabata.

Sai dai a nasu bangaren sojojin kasar sun ce suna kai hare-hare ne kan mayakan sa-kai na Rohingya, sun kuma musanta aikata ba daidai ba da kisan fararen hula.

A ranar 25 ga watan Agusta ne aka fara tashin hankalin, amma ya fi kamari a watan da ya wuce a lokacin da 'yan Rohingya suka kai hari kan ofishin 'yan sanda da ke Rakhine tare da hallaka jami'an tsaro 12.

'Yan Rohingya da suka yi hijira kasar Bangladesh, sun ce sojojin sun mayar da martani ta hanyar kashe su, da kona musu kauyuka da far wa fararen hula tare da tasa keyar wasu domin ficewa daga kasar.

Su dai 'yan Rohingya ba su da takamaimai kasar da za su kira ta su, saboda Myanmar ba ta dauke su a matsayin 'yan kasa ba; ta dai ce fatake ne da suka shiga kasar tare da samun wurin zama.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Mista Zeid, ya kara da cewa abin da ke faruwa a jihar Rakhine ya bayyana karara bai dace ba kisan wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Ya kara da bayyana ba za a magance matsalar ba idan har gwamnatin Myanmar ba ta tsoma baki ba, tare da bai wa sojoji izinin dakatar da budewa mutanen wuta. Ya kuma ce hukumomin kasar sun ki amincewa kungiyoyin kare hakkin bil'adama da 'yan jarida da kungiyoyin agaji shiga kasar dan gudanar da bincike.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa lallai an kona kauyukan 'yan Rohingya, da kashe su babu gaira ba dalili, hatta wadanda ke tserewa daga kasar bin su ake yi ana harbewa.

Wani mutum da wakilin BBC ya tattaunawa da shi cikin zubda hawaye ya shaida ma sa 'a kan ido na aka hallaka dana, da matarsa har da jikata, kuma babu abin da zan iya yi akai''.

"Ina kira ga gwamnatin Myanmar ta kawo karshen hare-haren da sojojin ke kai wa musulmin, ta kuma taimakawa tsirarun musulmin rage radadin galin da suke ciki, an kona musu gidaje, an lalata amfanin gona, don abin da suke da shi na bukatun yau da kullum an tilasta musu barin shi. Wannan zalunci ne karara da take hakkin bil'adam'', inji Zeid.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Kiyasi na baya-bayan nan ya nuna mutane 313,000 suka tsere daga myanmar zuwa kasar Bangladesh.

Kiyasi na baya-bayan nan ya nuna mutane 313,000 suka tsere daga Myanmar zuwa kasar Bangladesh. Hukumomin agaji sun ce mutanen na tsananin bukatar taimakon abinci, da ruwan sha, da magani, da matsuguni, kai har da abin da za su suturce jikinsu.

Kasar Bangladesh dai tuni ta dauki nauyin dubban musulman Rohingya da suka yi gudun hijira kasar, kuma sansanonin da aka kafa na 'yan gudun hijira sun cika makil ya yin da ake samun karuwar mutanen da suke tururuwa sansanonin, wasu daga ciki na kwanciya a sararin Allah duk da irin ruwan saman da ake shekawa.

Masu aiko da rahotanni sun ce, mutane na bin layin karbar abincin da ake ba su da bai wuce loma hudu ba, kuma akan idon su wani tsoho da ya galabaita da yunwa, da kishirwa da kumawahalar tafiya ya yanke jiki ya fadi a layin karbar binci.