Yadda yakin Syria ya gigita namun daji
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kun san yadda yakin Syria ya gigita namun daji?

Likitan dabbobi Amir Khalil, ya tafi yankunan da ake yaki don ceto dabbobin da suka yi saura a gidan ajiyar namun daji.

Da yawan su sun shiga firgici sakamakon yawan harbe-harbe da suke ji da kuma rashin abinci.

A nan mun yi duba ne kan bulaguron da aka yi da dabbobin, da suka hada da wata zakanya mai juna biyu, wadanda Amir da 'yan tawagarsa suka cece su, inda aka dauke su daga Syria zuwa Jordan ta hanyar Turkiyya.