Ko rashin bacci da wuri na sa yara dakikanci?

Makaranta
Bayanan hoto,

Dole dalibai su kwanta bacci karfe 9:30 na dare

Sabon shugaban makarantar ya sanya wata doka da yake shan suka a kanta, dokar da ya ce za ta karawa dalibai kaifin kwakwalwa.

Ana nuna damuwa kan yadda makarantar Great Yarmouth Charter Academy, ke kama da makarantar sojoji saboda tsauraran matakan da aka bullo da su wanda shugaban makarantar ya ce ya dauki matakin ne don zaburar da daliban yin karatu.

Cikin sabbin dokokin har da haramta musu rike wayar salula, matakin da iyaye suka nuna damuwa a shafukan sada zumunta da muhawara irin su Facebook.

Ga kuma batun kwanciya bacci da wuri da aka sanyawa daliban dokar, wadda ita ma ake ganin ta yi tsauri.

Sai dai mai magana da yawun hukumar makarantar ya ce sun dauki matakin ne don samawa dalibai nutsuwar yin karatu.

''An gagara ladabtar da daliban''

A cewar sabon shugaban makarantar Barry Smith, sakamakon jarabawar kammala makaranta na daliban shi ne mafi muni a kasar.

"Cikin dalibai 30 da ke cikin ko wanne aji, 21 da cikinsu sun kammala makarantar nan ba tare da sun ci darasin Turanci da Lissafi ba,'' in ji mista Smith.

Ya kara da cewa: ''A matsayina na shugaban wannan makarantar nan, ba zan nade hannu na zubawa dalibai ido ba tare da an ladabtar da su ba, na farko dai ba su da kunya, ga rashin mayar da hankali kan karatu. Wadannan dabi'u ne da suke yi a lokacin da ba ni ke jan ragamar makarantar ba.''

''Ba wai cin jarabawa kadai ake koya a makaranta ba, wuri ne na koyon tarbiyya. Kuma duk wani malami da ya san abin da ya ke yi zai so a ce dalibansa masu kokari ne.

"Ba wai kullum a yi ta karatu ba, a'a ai akwai lokacin shakatawa da gudanar da wasannin da makaranta ta amince da su.''

Bayanan hoto,

Iyayen dalibai sun nuna damuwa kan tsauraran matakan da ake dauka akan 'ya'yansu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kelvin Seal da ya ke da Da a makarantar, ya bude wani shafin Facebook inda iyaye ke zuwa suna tsokaci kan tsauraran matakan da makarantar ta dauka, ciki har da kayan da dalibai suke zuwa makaranta da su da kuma neman izinin da iyaye suke yi kafin ganin 'ya'yansu.

An dai shaidawa dalibai su kwanta bacci karfe 9:30 na kowanne dare, sannan su tashi daga bacci karfe 06:30 na safiya.

Sannan wadanda ke karyar rashin lafiya a lokutan karatu za a ba su bokiti su yi amai a ciki, maimakon yadda aka saba da ake cewa daliban su tafi daki su kwanta.

Mai magana da yawun wata kungiya da ke karfafawa mutane gwiwa, James Goffin ya yi tsokaci kan hakan.

''Abin takaicin shi ne an yi ta yada jita-jita da babu tushe balle makama da ake wallafawa a shafukan sada zumunta, wanda iyayen yaran ke fargaba akan sabbin dokokin da makarantar ta kafa''.

Wasu muhimman takardu da BBC ta gani, sun nuna irin horon da makarantar za ta dinga yi wa daliban da aka samu da aikata wani laifi da hukumar makarantar ta haramta.

Takardun dai sun kai shafi 22, kuma cikin abubuwan akwai;

  • Duk dalibin da ya yi magana, ko surutu, ko damun mutane da buruntu, ko bude littafi kafin a ba shi izini, ko kallon wani dalibi, ko waiwayen baya, ko kallon wani wuri daban a lokacin da malami ke cikin aji to za ka fuskanci hukunci.
  • Ba a amince ko wanne dalibi ya tashi daga kujerar zamansa ba tare da neman izini daga malaminsu ba.
  • Duk daliban da ke tafiya, dole su yi cikin tsari ta hanyar yin layi dogo ba mai fadi ba, sannan babu waiwaye haka nan ba tare da dalili ba, ba a amince dalibai su dinga yawo da jakar makaranta goye a bayansu ba.
  • Dole ne ko wanne dalibi ya nutsu ya saurari abin da malamai suke fada cikin aji. Kuma idan biron rubutun dalibi ya fadi kasa, ba zai dauka ba har sai malami ya bashi izini.
  • Malamai ba sa fita daga aji, don zuwa bandaki yin wata lalura suna amfani da wani salo ne su fita. Don haka ana bukatar dalibai suma su koyi irin salon ta yadda babu mai sanin abin da za su yi.
Bayanan hoto,

Steven Homes ya ce 'yarsa tana kuka take rokonsa don Allah kar ya mayar da ita wannan makarantar

Steven Holmes, mahaifin wata dalibar makarantar ce, ya ce 'yarsa ta dawo daga makaranta da hawaye wani na bin wani kuma wannan ce ranar farko da ta fara zuwa makaranta ta ce tun da ta je ake mata tsawa har aka tashi, don haka ba ta son komawa makarantar.

Ya kara da cewa: ''Hukumomin makarantar za su gudanar da babban taron iyayen yara, wanda za a hadu a tattauna sabbin manufofin makarantar Great Yarmouth Charter Academy, iyayen da suke ganin za su amince da dokokin sai su fada wadanda ba za su yi ba kuma ina ganin babu tilas.''