Kalli bikin baje kolin Hotuna a Abuja
An fara babban bikin baje kolin hotuna na nahiyar Afirka a Abuja, wanda za a kwashe kwana biyar ana yi. Ga wasu daga cikin hotunan da aka baje kolinsu a ranar Talata.

Taken bikin na shi ne Abuja International Photo Fest 2017
Masu sana'ar daukar hoto daga ciki da wajen kasar ne suke halartar bikin
A ranar Laraba ne taron zai kai kololuwarsa, inda za a gabatar da jawabai
Hotunan da aka bale kolinsu sun tabo bangarori daban-daban na rayuwar al'umma
A ranar Asabar ne za a yi bikin Gala, inda 'yan wasa musamman masu wasan bankwarci za su nishadantar da jama'a
Cikin hotunan da ake baje kolinsu har da hotunan sarauta
Har ila yau akwai hotunan da ke nuna muhimmancin ilimi musamman ga yara kanana
Akwai kuma hotunan da ke nuni da sana'o'in 'yan Afirka iri daban-daban