Giwayen Afirka sun bullo da dabarar kariya daga maharba

Giwaye a dawa

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

A duk minti 15 ana kashe giwa daya daga cikin 500,000 da ke Afirka

A wani bincike da aka yi a Kenya a gano cewa giwayen Afirka sun bullo da wata dabara ta amfani da duhun dare domin kare kansu yayin da aka tsananta farautarsu.

Masu bincike daga kungiyar kare giwaye ta, Save the Elephants, a Jami'ar Twente a kasar Holland, sun gano hakan ne bayan da suka rika bibiyar wasu gomman giwaye tsawon shekaru a dazukan arewacin Kenya.

Masanan sun gano cewa yayin da farauta ta tsananta, sai giwayen suka rika yawo da daddare fiye da yadda suka saba yi da rana.

Sannan kuma sun gano cewa a cikin giwayen ma mata su ne suka fi yin hakan fiye da maza, watakila saboda kare 'ya'yansu.

Masu binciken sun ce za a iya amfani da bayanan wajen inganta matakan rage farautar giwaye.

Masu bincike daga kungiyar kare giwaye ta, Save the Elephants, a Jami'ar Twente a kasar Holland, sun gano hakan ne bayan da suka rika bibiyar wasu gomman giwaye tsawon shekaru a dazukan arewacin Kenya.

Masanan sun gano cewa yayin da farauta ta tsananta, sai giwayen suka rika yawo da daddare fiye da yadda suka saba yi da rana.

Sannan kuma sun gano cewa a cikin giwayen ma mata su ne suka fi yin hakan fiye da maza, watakila saboda kare 'ya'yansu.

Bincike ya nuna kusan duk minti 15 ana kashe giwa daya a dazukan Afirka, abin da ke nuna kenan a kullum ana kashe kusan 100 a duk rana.

Wannan na nuna cewa yawan giwayen da aka kiyasta akwai a Afirka su kusan 500,000 suna raguwar da za a iya wayar gari sun kare a nahiyar.

Masu binciken sun ce za a iya amfani da bayanan da aka gano na dabarar da giwayen ke amfani da ita a yanzu ta yawo da daddare, maimakon rana wajen inganta matakan rage farautarsu.