Shugabar Myanmar ba za ta halarci zaman MDD na shekara ba

An dauki hoton a ranar 21 ga watan Satumba 2016 , a lokacin da Aung San Suu Kyi ke yi wa taron Majalisar Dinkin Duniya a karo na 71 a Manhattan, da ke Amurka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Aung San Suu Kyi a lokacin da ta ke yi wa taron zaman Majalisar Dinkin Duniya a bara

Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, ba za ta halarci babban zama na Majalisar Dinkin Duniya da za a yi a mako mai zuwa, saboda rikon sakainar kashin da ake zargin ta yi kan halin da tsirarun musulmi na kabilar Rohingya, da kuma kin daukar mataki don kare su.

Musulmi 'yan Rohingya 370,000 akai amannar sun tserewa jihar Rakhine, zuwa makobciyar kasar Bangladesh, tun bayan barkewar rikici a yankin a watan da ya gabata, inda aka kona kauyukan da musulmin ke zaune.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta zargi gwamnatin da zuba ido ana kokarin shafe wata al'umma daga doron kasa.

A nasu bangaren sojojin Myanmar sun ce suna yaki ne da 'yan gwagwarmaya na Rohingya, tare da musanta kai hare-hare kan fararen hula.

'Yan kabilar Rohiongya marasa rinjaye na zaune ne a jihar Rakhine da mabiya addinin Buddha suka fi yawa, sun dade suna fuskantar cin zarafi da gallazawar da ake yi musu.

Suna fuskantar hare-hare saboda a cewar 'yan kasar, Rohingya ba 'yan kasa bane sun shigo kasar ne a matsayin fatake ko 'yan cirani da suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba, don haka ba za a ba su shaidar zama 'yan kasa ba.

Gaba kadan ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman kan halin da 'yan kabilar Rohingya su ke ciki.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ko Shugaba Aung San Suu Kyi ta sauya tunani?

Ana dai sa ran Mis Suu Kyi za ta shiga tattaunawar da za a yi kan batutuwa da dama da Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta a birnin New York na Amurka, da za a fara a ranar 19 zuwa 21 ga watan nan.

Mai magana da yawun gwamnatin Myanmar Aung Shin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, watakila shugabar na da batutuwa masu muhimmanci da ya kamata ta warware da suka shafi kasar dalilin kenan da ba za ta halarci zaman ba.

Ya kara da cewa ba ta taba jin tsoro ko karaya kan sukar da ake mata ba, sannan babu wata matsala da ta taso da gwamnatinta ta gagara magancewa.

A jawabi na farko da ta taba yi wa zaman Majalisar Dinkin Duniya a bara a irin wannan lokaci, ta yi kokarin kare gwamnatinta kan namijin kokarin da ta ke yi don ganin an magance rikici da barazanar da musulmin kabilar Rohingya ke ciki a kasarta.

Ana yabawa Shugaba Suu Kyi wadda ta taba daukar lambar yabon zaman lafiya ta Nobel, da kuma aka taba yi mata daurin talala na shekara 15, saboda gwagwarmayar da ta ke yi na tabbatar da Dimukradiyya ta samu gindin zama a kasar Burma, da gwarzuwa kuma jaruma mai magana daya da ta samu jan ragamar kasar duk da irin kalubalen da ta fuskanta.

Asalin hoton, Getty Images

Masu goyon bayan gwamnatin Mis Suu Kyi a kasashen yammacin duniya, na sukar lamirinta a yanzu saboda gazawa da kawo karshen rikicin kabilanci da na addini da ke faruwa a jihar Rakhine.

Ko a makon da ya gabata ta ce zuki ta malle ce da kuma zuzuta halin da ake ciki a kasar.

Sauran 'yan uwanta da suka karbi lambar yabon ta Nobel ciki har da jagoran mabiyar addinin Buddha Dalai Lama, da Archbishop Desmond Tutu na kasar Afurka ta Kudu, da Malala Yousafzai, sun yi kira ga Mis Suu Kyi ta kawo karshen kashe-kashen mutanen da ake yi a kasarta.

Wai me ke faruwa ne a jihar Rakhine?

Kiyasi na baya-bayan nan na adadin 'yan Rohingya da suka tsere daga muhallansu ya fara ne daga ranar 25 na watan Agusta da ya wuce, sakamakon hare-haren da sojoji da 'yan sanda ke kai musu.

Wadanda suka tsere sun ce sojojin Myanmar sun maida martani kan wadanda ba su san hawa ba bare sauka, kan harin da wasu da ake zargin 'yan gwagwarmaya na kabilar Rohingya ne suka kai wasu ofisoshin jami'an tsaro.

Wani dattijo ya shaidawa BBC cewa a kan idonsa aka hallaka dansa, da surukarsa da kuma jikansa, daman tun wancan rikicin na farko aka hallaka mai dakinsa.

Iyaye mata na goyo da yaro a baya, sannan jaye da wasu, ga fagon kaya dauke akansu, cikin gajiya da galabaita, wannan shi ne yadda hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta ke wallafawa.

Wani hoton mai tashin hankali, shi ne na wani tsoho da kwale-kwalensu ya kafe a cikin ruwa, ya yi shahadar dauko wasu yara uku, daya a kafadarsa, biyu a janye a hannunsa.

A kan nuno hotunan mata zaune sun hada kai da gwiwa, cikin tsananin bukatar taimakon ruwa da abinci, ya yin da yara kanana mata da maza ke zaune babu suturar kirki a jikinsu saboda an fito cikin dimuwa da neman tudun muntsira.

Hatta jarirai ban da kuka babu abinda suke tsanyarawa, babu suturar da ta rufe su ruf, ga ruwan sama da ake shekawa kamar da bakin kwarya, sannan iyayen ba su ci abincin da zai kawo musu isasshen ruwan nonon da jariran za su sha.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mahaifiyar wannan yarinya Kalima mai shekara 10, ta ce sojojin Myanmar ne suka soka mata wuka

Sun ce an yi ta kai musu hare-hare babu kakkautawa, ta inda suke ganin tamkar so ake a share su daga doron kasa baki daya.

Sai dai babban wakilin Myanmar a Majalisar Dinkin Duniya, ya dora alhakin abubuwan da ke faruwa kan tsirarun musulmi na kabilar Rohingya da ke yankin Rakhine da ya ce suna ta da zaune tsaye, da kai wa jami'an tsaro hare-hare kuma gwamnati ba za ta amince da ayyukan ta'addanci ba.

Duk da cewa an tsaurara matakan tsaro a yankin Rakhine, ta yadda 'yan jarida da kungiyoyin agaji suka gagara isa don taimaka musu. Rashin kyawun hanya na daya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta ta isa wurin su, sai kuma uwa uba kankane ko'ina da sojojin Myanmar suka yi don ganin ba a isa yankin ba.

Wakilin BBC Jonathan Head na daga cikin tsirarun 'yan jaridar da suka samu damar shiga Jihar Rakhine bisa jagorancin wakilan gwamnati, ya rawaito cewa an kona kauyuakn da musulmai ke ciki, yayin da wadanda ba a kona ba kamar kufai babu kowa a ciki.

Mata sun zubar da kayayyakinsu, ga kayan yara a yashe a kasa, maza sun zubar da kayan aikinsu na noma, yayin da amfanin gonar ma an gudu an bar shi.

Wani abin mamakin shi ne akwai jami'an tsaro tun daga soja har 'yan sanda amma babu wani yunkuri da suka yi na hana hakan.

Yayin da musulmin Rohingya kusan 400,000 suka tsere daga muhallansu, Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira sun cika kasar Bangladesh da tafi makobtaka da Myanmar, sannan ko a baya kasar ta dade da daukar wasu 'yan gudun hijirar.

A halin da ake ciki wasu dubban 'yan Rohingya su na gararanba a sansanin da aka kafa na cikin kasar, cikin fargaba da tashin hankalin rashin sanin makomarsu.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shaheda mai shekara 40 na karbar magani sakamakon konewar da ta yi a lokacin da sojoji suka cinnawa gidanta wuta