Dalibar jami'a ta dambata da barayi

Na'urar daukar hoto ta CCTV ta dauki bidiyon dukkan abin da ya faru

Asalin hoton, Sowetan Live Twitter

Bayanan hoto,

Na'urar daukar hoto ta CCTV ta dauki bidiyon dukkan abin da ya faru

Kafar yada labarai ta intanet ta Sowetan Live ta ruwaito cewa, wata dalibar jami'a a Afirka Ta Kudu, ta dambata da barayi wadanda suka so kwace mata komfutar da ke dauke da aikin binciken da take yi don kammala digirinta na biyu.

A karshen wannan watan ne za ta gabatar da aikin binciken nata a gaban malamanta.

Dalibar 'yar shekara 26 Noxolo Ntuli, da ke karatun likitanci a Jami'ar Johannesburg, ta samu horo a wata cibiyar koyar da kare kai, bayan da aka taba yi mata fashi a wannnan yankin.

Sai dai a wannnan karon ta yi kokarin fatattakar barayin ne, wadanda ba su kwace komai ba sai jakar abincinta kawai.

Kafar yada labaran ta ruwaito cewa, mutane da dama sun yaba da jarumtakarta.

Rahoton ya kara cewa, na'urar daukar hoto ta CCTV ta dauki bidiyon dukkan abin da ya faru, kuma an kama mutanen uku.

Miss Ntauli ta fadawa kafar yada labaran cewa, 'Ina fatan doka za ta yi aikinta'.

Ta kara da cewa: 'Ina farin cikin kama su da aka yi, kuma ina fatan za a tuhume su da kokarin sace mutum da yin fashi.'

Dalibar dai ta yi hakan ne domin tsare martabar binciken da take yi din, wanda dalibai kan dauki lokaci mai tsawo suna yi.