Hotunan katafariyar gonar kaji da Buhari ya kaddamar a Kaduna

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da daya daga cikin manyan gonakin kiwon kaji a Afirka wacce aka gina a jihar Kaduna.

Gonar Olam Kaduna
Bayanan hoto,

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da daya daga cikin manyan gonakin kiwon kaji a Afirka wacce aka gina a jihar Kaduna.

Bayanan hoto,

Kamfanin na kiwon kaji na kasar Singapore mai suna Olam wanda aka sanya jarin Dala Miliyan 150 zai samar da kananan kaji miliyan 1.2 a ko wanne mako.

Bayanan hoto,

Ana kuma sa ran samar da gonar zai rage shigar da kaji da dangogin su daga kasashen ketare.

Bayanan hoto,

Gonar za ta dinga samar da kaji da abinci kaji da kwai ga manoma a ciki da wajen jihar Kaduna

Asalin hoton, Nigerian Presidency Twitter

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da bude gonar, inda ya je har garin Kadunan a ranar Talatar.

Asalin hoton, Nigerian Presidency Twitter

Bayanan hoto,

An shirya gagarumin biki don bude wannan gona, inda gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya karbi bakuncin taron.

Asalin hoton, Kaduna State Govt

Bayanan hoto,

Ministan aikin gona na Najeriya Audu Ogbeh ya ce kafa kamfanin wani yunkuri ne na inganta aikin noma a kasar, 'wanda ya fara samun alamun tagomashi.'

Asalin hoton, Kaduna State Govt

Bayanan hoto,

"Mun fara ganin matasa na barin manyan birane don komawa garuruwansu su shiga aikin noma, bayan da suka fahinmci amfanin hakan," in ji Mista Audu Ogbeh.

Asalin hoton, Olam Farms Twitter

Bayanan hoto,

Ana sa ran yawan bukatar naman kaji ga 'yan Najeriya zai rubanya sau 10 nan da shekarar 2040.