Mata 'yan shi'a sun yi zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

Mata 'yan shi'a

Wasu dumbin mata daga Kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a a Nigeria, sun bukaci hukumomi a kasar da su gaggauta sakin Shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Matan wadanda suka gudanar da zanga-zanga a ranar Laraba a habarar hukumar kare hakkin bil'adama da ke Abuja, sun ce sau da dama kotu a kasar na bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky amma har yanzu gwamnatin kasar ta ki yin biyayya ga hukuncin kotun.

Malama Maimuna Bintu Husseini, na daya daga cikin matan ta kuma yi wa Ishaq Khalid karin bayani kan dalilinsu na shirya zanga-zangar:

Bayanan sauti

Bayanin Maimuna Bintu Husseini kan zanga-zangar 'yan shi'a

Bayanan hoto,

Wasu matan sun je wajen zanga-zangar da 'ya'yansu