Ta yaya talakawa za su ginawa gwamnati hanya?
Ta yaya talakawa za su ginawa gwamnati hanya?
A ranar Alhamis ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin sayar da takardun lamuni na Sukuk wadanda babu kudin ruwa a kansu.
A cewar jami'ai, wannan shiri zai taimaka wurin samar da kudaden da za a cike gibin da ake fama da shi a kasafin kudin kasar domin gudanar da wasu manyan ayyuka da suka hada da gina hanyoyi.
Wadanda suka zuba jarinsu a wannan tsari za su ci riba ne ta hanyar kudin da za a rinka biyansu sakamakon amfani da wadannan hanyoyi.
Wannan ne dai karon farko da Najeriya ke kaddamar da wannan tsari na Sukuk.
Malam Muhammad Adamu ma'aikaici ne a hukumar kula da basuka ta Najeriya, kuma ya yi wa Naziru Mikailu karin bayani kan shirin.
Sai ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron hirar.