Yadda na ceto 'ya'yana daga hannun IS a Syria'

  • Daga Steven Rosenberg
  • BBC News, Dagestan a Kudancin Russia

A lokacin da ya ke zaune a bayan gidansa, kawai sai Artur Magomedov ya fara tuno wani lokaci da ya shiga tashin hankalin da bai taba samun kansa a ciki ba.

"Matar kawuna da dan uwana sun kawo min ziyara, sun kuma shaida min matata ta zo ta dauke 'ya'yanmu."

Ba tare da ta shaida masa ba ta zo ta dauke 'ya'yansu guda biyu, Fatima mai shekara 10, da Maizarat dan shekara uku, inda ta wuce da su kasar Turkiyya, daga nan ta tsallaka iyakar kasar da Syria daga nan ne kuma ta shiga kungiyar masu tsattsauran ra'ayin musulunci ta IS.

"Kawunta da dan uwanta babu wata alamar bacin rai a tattare da su. Amma na shaida musu, ''Lallai ba zan lamunta ba,'' waya ba ta izinin daukar min 'ya'ya ta yi tafiya da su ba tare da izinina ba?''

Bayanan hoto,

Yankin Dagestan daya ne daga cikin yankunan talakawa su ke zaune a Rasha, kuma yawancin masu fafutukar jihadi anan su ke zaune.

A yankin Dagestan, matar Artur ta rungumi tsattsauran ra'ayi hannu bibbiyu daga 'yan kungiyar IS, wadanda suka yi alkawarin ayyana doron kasa baki daya karkashin kasar Musulunci.

Ba ita kadai ta samu kanta a cikin wannan hali ba. Wannan yankin na kasar Rasha cike yake da sabbin shiga kungiyar IS da ake horas da su.

A kalla akwai mutum kusan 1,200 da aka horas da su kuma suka shiga kungiyar. A iya kiran wurin kebantacciyar makarantar horas da mayakan kasar musulunci.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Artur ya kuduri aniyar ceto 'ya'yansa.

Tafiya mai nisa har zuwa matattarar IS

Ba shi da isassun kudin guzuri, amma sai da ya ci bashin kudi ya tafi birnin Santanbul na Turkiyya. A can ne ya dan kwana biyu ya kuma samu wani mutum a asirce da ya yi masa bayanin hanyoyin da zai bi don isa inda ya nufa.

''Daga birnin Santambul, mun yi tafiya mai tsaho a mota har muka kai garin Gaziantep da ke kudancin Turkiyya. Anan na samu wasu iyalai da suka fito daga Checheniya, da kuma wasu mutum uku da suma abokan tafiyata ne.''

"A kalla mun sauya mota sau biyar, kafin muka isa iyakar kasar Turkiyya da Syria. Anan muka sake haduwa da wasu takadarai da suka shirya baki dayan tafiyar.''

"Wato idan kana son tsallake iyakar a kalla sai ka yi gudun mita 200, kuma gudu na gaske za ka yi don ya fi kama da ceton rai, haka muka yi ta sheka gudu rakwacaf-rakwacaf da kaya ga jaka kuma goye a bayana.

"Ai masu gadin iyakar su kuma na ta barin wuta idan sun ji motsi ko sun hango wani abu daga nesa idan ba ka da rabo su bindige ka. Wato a lokacin da nake gudu kamar zuciyata za ta fado kasa saboda bugawa.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Babbar kasada ce tsallaka iyakar Turkiyya da kasar Syria

"A lokacin da na isa yankin da IS suka fi rinjaye. Wasu sojoji na zaune cikin wata mota suna jira su dauke mu. Fuskokinsu a murtuke ba sa ko fara'a, muka shiga motar suka falla da gudu ba mu tsaya ko ina ba sai Jarablus, inda za a kara tantance mu kafin a kara gaba.''

Anan ne Artur ya samu cikakken bayanin inda 'ya'yansa suke. Anan ne ya samu wani sakon kar-ta-kwana daga mijin 'yar uwarsa da ya kara masa wa'adin biza, wadda ita kanta kanwar tasa ta shiga kungiyar IS.

''Abin da ya rubuta min shi ne: 'Ni mutum ne mai adalci, amma kai ba a maka adalci ba. Dalilin da ya sa na neme ka kenan.''

Bayanan hoto,

Taswirar yadda Kasar Turkiyya da Rasha su ke

Wannan dan uwa na Artur ya shaida masa matarsa da 'ya'yansa suna wani gari wai shi Tabqa. Bai yi kasa a gwiwa ba ya tafi nemansu.

"A lokacin da yaran suka ganni, farin ciki ya baibaye su, babbar 'yata Fatima tana sanye da bakar doguwar riga da ta rufe mata baki dayan jikinta, da kuma hijabi.

Ita kuma Maizarat da yake har yanzu yarinya ce tana sanye da ainahin kayan da take sanyawa a lokacin suna gida.''

''Ban samu matata a gida ba a lokacin da na je, amma ba a dade ba ta fyallo da gudu da ta samu labarin zuwana, anan ta gane tana cikin hadari,'' in ji Artur.

Ba tare da bata lokaci ba, wata kotun addinin musulunci ta bai wa Artur izinin daukar 'ya'yansa. Sai dai kuma an haramta masa fita da su daga kasar musuluncin, idan yana son yin hakan sai dai ya tsere da su kenan.

Da tsakar wani dare Artur ya sabi Maizarat 'yar shekara uku, ya kama hannun Fatima suka gudu, ba su tsaya ba sai a iyakar Syria da kasar Turkiyya.

"Mun kwanta a kasa muka yi ta mirginawa, har muka tsallake layin dogo na jirgin kasa, mai nisan kilomita 70.

Bayan mun dan nunfasa na sake sabar Maizarat a kafada na cewa Fatima ''Mu gudu,'' kafin na rufe baki ta yanki hanya da gudu, ban taba ganin tashin hankali irin wannan ba.''

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar IS ta rasa iko da yankin Tabqa, sai yakin ya nausa yankin Raqqa

"A yayin da muke gudu ne wandona ya yage a jikin wayar shinge ta tsaro, ita kuma Fatima rigarta ta yage. Maizarat kuma ta fara kuka. Ban san yaya aka yi na samu karfin halin ci gaba da tafiya ba

"Mun tsallake kan iyakar muna faduwa muna tashi. Masu gadin kan iyakar Turkiyya ba su fi mita 50 ba tsakaninmu da su, muna jiyo harbe-harbensu.

"Muna jin harsashai na wucewa ta kanmu. Da durkuso muka samu muka sha. A yayin da na fahimci na tsira ne na fara hango hasken taurari da farin wata, sai na ji kamar a aljanna nake.

Artur da 'ya'yansa sun samu isa Istanbul, a inda ofishin jakadancin Rasha ya taimaka musu komawa gida.

Bayanan hoto,

The two girls were issued travelled documents by the Russian consulate and allowed to return home

Shin ina matar Artur?

"Ban san inda take ba gaskiya, ban kara jin duriyarta ba, ta bi son zuciyarta ta zabi shiga kungiyar IS don haka kowa sai ya yi rayuwarsa,'' in ji Artur.

Mahaifiyar Artur ta shaida min cewa yawancin mutanen kauyensu, sun shiga kungiyar IS.

Shin me ke daukar hankalinmabiya addinin Kibdawakan zuwa Syria?

Yankin Dagestan daya ne daga cikin yankunan da talauci ya yi kaka gida, da rashin aikin yi, da rashin abababen more rayuwa har ma da rashin makarantu masu kyau a kasar Rasha.

Wannan dalilin yana daga cikin abin da ya janyo duk wasu masu tsattsauran ra'ayi da 'yan ta'adda yin kaka gida a wurin.

Bayanan hoto,

"Za mu kare yankin mu daga 'yan ta'adda, ba mu amince da ayyukan ta'addanci ba" Wannan shi ne babban allon da aka kafa a yankin Dagestan

Marat, matashi ne da ya gudu daga gida, ya shiga kungiyar IS amma daga baya ya tsere, a yanzu yana rayuwa ne a boye.

A lokacin da muka hadu da shi ya shaida min cewa hure masa kunne aka yi da dadadan kalamai da tanadin rayuwa ingantacciya. Kuma ta shafin Internet aka rinjaye shi, ya rabu da iyayensa da matarsa dauke da juna biyu, ya shiga kungiyar jihadi a Syria.

Ya shaida ma na cewa: ''Suna yi mana wa'azin da yake kashe zukatan masu karantawa ko saurara, ka samu shauki da karsashi babu abin da ka ke so face ka ganka a tsakiyar filin daga kana aikin Allah, kamar yadda suke fada,'' in ji Marat.

"'Don me kana musulmi za ka zauna a gida? Fito ka yi aikin Allah. wadannan na daga cikin kalmomin da muke ganin an wallafa a shafukan sada zumunta.

"Daga nan baka samun kwanciyar hankali sai ka tafi. Nima hakan ce ta same ni''. Marat ya fada cikin zub da hawayen nadama.

"Sai daga baya na gano, na tafka babban kuskure. Na fahimci cewa babu wani abu da ya danganci addini da ake yi a wurin. Kawai musulmai ne ke yakar 'yan uwansu musulmai saboda son zuciya.''

'Ku rufe masallacin, ku kuma matasa ku bar wurin nan'

Bayanan hoto,

Dagestan na cike da kalubalen yaki tsakanin matasa da kananan yara da ba su san inda za su kama ba

A wani gari mai suna, Shamkhal, na hadu da wani mai suna Shamsutdin Magomedov ya shaida min wani masallaci da suke yin salla a unguwarsu, a yanzu 'yan sanda sun rufe shi.

''Watakil hakan bai rasa nasaba da mutum biyar zuwa shida da muke sallah tare kullum, an daina ganin su daga baya aka ce sun tafi kasar Syria don shiga kungiyar Jihadi. Amma duk da hakan ban ga dalilin da za su rufe mana masallaci ba, hakan ba zai kawo karshen matsalar ba ai,' in ji shi.

"A duk lokacin da aka ce akwai matasa anan tare da mu, za mu sanya ido sosai a kansu, amma an kama masallaci an rufe, matasan sun tarwatse ta yaya za ka gansu bare ka gano sun sauya dabi'a, ba mu san inda suke zuwa ba ko mutanen da suke mu'amala da su,'' in ji Shamsutdin.

Da na koma bayan gidan Artur Magomedov, karamar 'yarsa Maizarat tana zaune a kan wata kujera karama tana kallon mu.

Na kuma tambayi Artur wacce irin illa zaman da 'ya'yansa suka yi a kasar da 'yan IS ke cin karen su babu babbaka ta shafi rayuwarsu, rayuwa a Syria tare da mahaifiyarsu, daga baya kuma ya kubutar da su, wacce rayuwa suke yi?

''Abin da zai baka mamaki, karamar 'yata Maizarat, ta tambaye ni kowa yana tare da mahaifiyarsa su ina ta su uwar?

Na san yaran har yanzu suna gaisawa da mahaifiyarsu ta shafin sada zumunta, tun da Fatima babba ce da wayonta, na fada musu su daina neman ta, na san ban isa raba Da da mahaifi ba. Kuma ko yaya ta ke ai mhaifiyarsu ce ban isa sauya musu ita ba. Kuma na san tabbas suna kewarta,'' in ji Artur cikin jimamami da rashin walwala.

Bayanan hoto,

Wannan taswirar tana nuna yadda IS ta karbe iko da wasu yankunan kasar Syria da Iraqi. An kuma dauki hoton ne a ranar 2 ga watan Satumbar 2017