Saudiyya na dirar mikiya kan 'bijirarrun malamai'

Sheikh Salman Odah

Asalin hoton, FACEBOOK/@SALMANALODAH

Bayanan hoto,

Hukumomin Saudiyya ba su ce uffan game da batun tsare malaman ba

Hukumomin Saudiyya sun kama malaman addini fiye da 20, a wani mataki da ake ganin murkushe masu bijire wa gwamnati ne, a cewar 'yan fafutuka.

Fitattun malaman addinin musulunci Salman al-Odah da Awad al-Qarni na daga cikin mutanen da aka ba da rahotannin cewa ana tsare da su tun a karshen makon jiya.

Ya zuwa yanzu hukumomi ba su tabbatar da wadannan bayanai ba.

Sai dai a ranar Talata, kafar yada labaran Saudiyya ta ce ana tsare da gayyar wasu mutane da ke aiki a madadin "kungiyoyin kasashen waje da ke yunkurin kawo cikas ga tsaron masarauta."

Ba a yi bayani kan ko su wane ne daidaikun mutanen ba, amma dai wata majiyar tsaro ta fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ana zargin mutanen ne da "satar bayanan sirri da kuma hulda da wasu cibiyoyin kasashen waje ciki har da Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi".

Gwamnatin Saudiyya na daukar Kungiyar a matsayin ta 'yan ta'adda, kuma wani bangare ce a dambarwar da ake ciki tsakanin masarautar da makwabciyarta Qatar.

Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da kuma kasar Masar duk sun katse kowacce irin hulda da Qatar a watan Yuni, bayan sun zarge ta da mara baya ga kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Qatar ta amsa cewa ba shakka tana tallafa wa kungiyar 'Yan'uwa Musulmi, amma dai ta musanta ba da taimako ga masu jihadi da ke da alaka da al-Qaeda ko kuma kungiyar ISIS.

Wani mai fafutukar kare hakkin dan'adam da ke zaune a Burtaniya, Yahya al-Assiri ya fada wa mujallar Wall Street cewa jami'an da suka kama Sheikh Salman Odah a Riyadh ne da daren Asabar sun furta rashin bayyana goyon bayansa a kan manufar Saudiyya ga kasar Qatar a matsayin dalili.

A ranar Juma'a, Salman Odah ya bayyana fata a shafinsa na Twitter cewa zantawa ta wayar tarho da Yarima mai jiran gadon Saudiyya Mohammed bin Salman da Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al Thani suka yi, manuniya ce cewa an kusa kawo karshen rikicin.

Sai dai, jami'an Saudiyya daga bisani sun ba da sanarwar cewa sun jingine duk wata tattaunawa da Qatar, inda suka zarge ta da "jirkita hakikanin gaskiya" a wata sanarwa dangane da hirar.

Sheikh Odah, wanda aka san shi a baya kan tsauraran manufofinsa na addini, an taba tsare shi a gidan yari daga 1994 zuwa 1999 saboda rajin da ya yi don samun sauyin siyasa, mashahurin malami ne da ke da mabiya miliyan 14 a Twitter.

Haka zalika, Sheikh Qarni, wanda aka tsare shi a birnin Abha da ke kudancin kasar, an ba da rahoton kiran da ya yi na samun kyautatuwar dangantaka da Qatar a shafinsa na Twitter, mai mabiya miliyan biyu.

A ranar Laraba, masu fafutuka sun raba jerin sunayen wasu jiga-jigai da suka yi imanin cewa ana tsare da su, ciki har da sauran malaman addini da dama da malaman makaranta da masu gabatar da shirye-shirye a talbiji da wani mawaki.

Wasu ba su da wata alaka karara ga tsaurin ra'ayin addini ko kuma tarihin nuna adawa ga masarautar Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya a lokaci guda kuma ta bukaci 'yan kasar su kai rahoton duk wani kalami a shafukan sada zumunta da ke yayata "akidun ta'addanci ko tsattsauran ra'ayi" ta hanyar wata manhajar waya da aka kaddamar bara.

Mai gabatar da kara na gwamnati ya tunasar da su a shafinsa na Twitter cewa "cutar da suna ko matsayin kasar" wani aikata "laifin ta'addanci ne".

Matakin murkushe masu nuna bijirewar ya zo ne bayan wata kungiyar 'yan adawa da ke kiran kanta "Tafiyar 15 ga watan Satumba" ta yi kiran gudanar da zanga-zangar lumana ranar Juma'ar nan don matsa wa hukumomi lamba wajen shawo kan fatara da bunkasa 'yancin mata da kuma sakin fursunonin siyasa.

Saudiyya dai ta haramta duk wata zanga-zanga a kasar.