Kashe Nnamdi Kanu sojin Nigeria suka zo yi - Bar Ejiofor

Nnamdi Kanu

Asalin hoton, Getty Images

Lauyan jagoran kungiyar masu rajin kafa Biafra a Najeriya, Barista Ifeanyi Ejiofor ya zargi rundunar sojin kasar da yunkurin kashe Mazi Nnamdi Kanu a gidansa.

Ya ce kungiyar za ta kai kara gaban kotu don bin kadin jinin 'ya'yanta da 'aka ritsa da su a wannan samame na babu gaira babu dalili.'

Sai dai, mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya, Burgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa zargin ba shi da tushe balle makama.

Ya ce sojoji ba su kashe kowa ba, hasali ma su ne aka ji wa wani sojansu rauni.

"Idan an kashe mutum daya, wane ne shi? Yaya sunansa? Ko daga sama ya fado? Ina aka kai gawarsa?"

Sai dai Barista Ifeanyi Ejiofor ya ce suna da shaidu na hotuna da bidiyo na aika-aikar da sojojin suka tafka, a cewarsa.

Ya yi zargin cewa shi a ganinsa sojoji sun je gidan Nnamdi Kanu ne, don halaka jagoran masu rajin kafa Biafra.

Ya ce yunkuri ne kawai na kashe shi, "Idan ba haka ba, fada min me suke yi lokacin da suke ta harbe-harbe a cikin dakinsa," in ji lauyan.

A cewarsa 'wasu sun mutu, wasu sun ji raunuka' sakamakon arangamar da aka yi ranar Lahadi 10 ga watan Satumba.

Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa dakarunta sun kai samame tare da kashe mutane a garin Afaraukwu mahaifar jagoran IPOB, Nnamdi Kanu.

Ta ce sojojinta na shirin fara wani atisaye ne a yankin, inda wasu tsegarun kungiyar suka datse hanya ga kwambar sojojin da ke zagaya birnin Umuahia na jihar Abia da yammacin ranar Lahadi, har ta kai ga jifa da duwatsu da kuma kwalabe.