Yadda Kwankwaso da Ganduje 'ke siyasar banga a Kano'

Masana harkokin siyasar Najeriya sun ce rikicin bangar da ya barke a siyasar Kano `yan kwanakin babban koma-baya, da ka iya rage kimar jihar a idon sauran jihohin Najeriya.

Artabu ya barke ne tsakanin tsagin Gandujiyya da na Kwankwasiyya, karkashin inuwar jam`iyyar APC mai mulki, lokacin hawan daushe, inda aka jikkata mutane da dama.

Jihar Kano, madubi ce ta fuskar siyasa ba da gaba ba, amma dawowar banga a jihar ta sa wasu na dasa ayar tambaya a kan ci gaban da demokradiyya ta samu.

Ku latsa alamar lasifika domin sauraron rahoton da Ibrahim Isa ya aiko mana: