Nigeria: Yadda 'yan arewa suka tafka asara a rikicin IPOB

Nigeria: Yadda 'yan arewa suka tafka asara a rikicin IPOB
'Yan arewa sun yi asara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan arewa sun yi asara mai yawa

'Yan arewacin Najeriya da ke zaune a kudu maso gabashin kasar sun ce sun tafka asarar rayuka da ta dukiya sakamakon rikicin da masu fafutikar kafa kasar Biafra suke yi a yankin.

Sun shaida wa wakilinmu na yankin Abdussalam Ibrahim Ahmed cewa an kashe mutanensu da dama da kuma kona dukiyarsu.

Sai dai jami'an tsaro sun ce ba a samu asarar rayuka ba kawo yanzu.