Hotunan bikin kammala horas da 'yan matan Chibok 106

A ranar Laraba da daddare ne aka yi bikin kammala horas da 'yan matan Chibok 106 da aka kwato daga Boko Haram a Abuja.

Bikin kammala horas da 'yan matan Chibok
Bayanan hoto,

A ranar Laraba da daddare ne aka yi bikin bikin kammala horas da 'yan matan Chibok 106 a Abuja, wadanda aka ceto daga hannun mayakan Boko Haram.

Bayanan hoto,

A yanzu dai gwamnatin Najeriya ta mayar da 'yan matan wajen iyayensu.

Bayanan hoto,

Fiye da 'yan mata 200 ne 'yan Boko Haram suka sace, amma suka saki 106 a shekarar data gabata.

Bayanan hoto,

Ko wacce daga cikinsu an danka mata akwati guda cike da sutura da sauran kayan amfani.

Bayanan hoto,

Gwamnatin wacce ta shiryawa 'yan matan da kuma iyayensu lafiyar cin abincin dare a ranar Laraba a Abuja, ta ce sai da aka kwantarwa da 'yan matan hankali tare da duba lafiyarsu, a wani shiri na maido da su cikin hayyacinsu da gyara dabi'unsu da gwamnati ta shirya, kafin mayar da su a hannun iyayensu.

Bayanan hoto,

Hajiya Aisha Jummai Alassan ita ce Minista mai kula da harkokin mata a Nigeria, ta kuma shaidawa BBC cewa gwamnati na ci gaba da tattaunawa da kungiyar Boko Haram din don sako sauran wadanda ke hannunsu.

Bayanan hoto,

A yanzu dai gwamnati za ta dauki nauyin karatunsu tun daga yanzu har su kammala jami'a a ABTI American University da ke Yola.

Bayanan hoto,

Gwamnati ta kuma ba su kwamfutoci da wayoyin hannu, baya ga haka kuma mutane masu hali sun ba su kyaututtuka da dama.