North Korea ta sake harba roka

Missile test

Asalin hoton, KCNA

Koriya ta Arewa ta harba wani roka daga babban birnin kasar Pyongyang wanda yayi gabas inji kafafen watsa labarai.

Japan ta ce da alama rokan ya bi ta kan sararin samaniyar kasarta, kuma ta gargadi 'yan kasar da su nemi mafaka.

Kasashen Koriya ta Kudu da Amurka na nazarin harba rokar na baya-bayan nan, inji kamfanin dillancin labarai na Yonhap.

A watan jiya ne Koriya ta Arewa ta harba wani roka wanda ya bi ta sararin samaniyyar kasar ta Japan, kuma gwamnatin kasar ta yi allawadai da abin da ta kira "gagarumin barazana" ga kasar.

Wannan lamarin ya zo kwanaki ne bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Koriya ta Arewar sabbin jerin takunkumi dangane da gwaje-gwajen makaman nukiliya da ta yi.

Fadar shugaban Koriya ta Kudu, Blue House, ta bukaci komitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya duba wannan batun cikin gaggawa.