Nigeria: 'A ajiye tsarin mulki a fuskanci gaskiya'

Map of Nigeria

Wani dattijon arewacin a Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi ya shawarci mahukunta su jingine batun tsarin mulki su fuskanci zahirin gaskiya game da ci gaban kasar dunkulalliyar kasa guda.

Ango Abdullahi Farfesa wanda shi ne mai magana da yawun Kungiyar Dattijan Arewa na wannan jawabi ne yayin da ake fuskantar tunzuri cikin yankin kudu maso gabashin Najeriya a baya-bayan nan.

Ya ce mafita guda ga Najeriya ita ce a fada wa juna gaskiya a jingine "maganar takarda" don tabbatar da makomar kasar.

"Ba maganar yaudara ba. Ba maganar, abin da ake kira tsarin mulki ba ne, a kan takarda.

Tsarin mulki yana kan takarda, wadanda aka yi dominsu suna nan a kasa. Su ne kuma ake fama da ra'ayinsu cewa ba za su yi zaman lafiya tare ba."

Dattijon ya zargi 'yan siyasar kasar da "munafunce-munafunce da kwane-kwane."

"Mu zauna a yi wannan magana, ba tare da munafunce-munafunce... irin wadanda shekarun nan ke nuna 'yan siyasa na yi ba.

Asalin hoton, AFP/AP

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ya ce a tunkari zahirin gaskiyar game da makomar Najeriya don tabbatar da jin dadin kowa da kowa.

"Wannan abin da muke kira Najeriya, zai yiwu mu ci gaba da zama irin yadda muke yi a yanzu? Ko kuma akwai wata dabara da za a shigar don samun jin dadin kowanne bangare?"

A cewarsa, tsarin mulki ba shi ne mafita ba, don kuwa Najeriya ta yi sauye-sauyen tsarin mulki a karo da dama amma an gaza samun masalaha.

Ya ce: "Ba kasar da ta yi taron sauya tsarin mulki kamar Najeriya ba tare da samun daidaito ba."

"Akalla, bayan tafiyar Turawa, mun yi taron tsarin mulki kamar shida ko bakwai, kafin ya tafi, ya yi guda uku, tara kenan. Amma har yanzu an ce kasa ba ta zauna da gindinta ba."

Farfesa Ango Abdullahi ya ce kamata ya yi a hau teburin tattaunawa don gano abubuwan da suka hana Najeriya zama da gindinta.

"Sai a zo a zauna...(don gano) wanne murhu ko murahu ne ke gocewa (har) tukunyar ke son ta fadi ta fashe."