Wasu abubuwa sun fashe a tashar jirgin London

Bag Hakkin mallakar hoto PA

Rundunar 'yan sandan London ta ce tana kallon harin da aka kai a wata tashar jirgin birnin a matsayin na "ta'addanci".

Wasu fasinjojin jirgin karkashin kasa na London sun ji raunuka bayan wani abu ya fashe a tashar District Line da ke kudu maso yammacin birnin.

An yi kiran 'yan sanda da likitoci da misalin 08:20 ranar Juma'a domin zuwa tashar jirgin da ke Parsons Green station a Fulham don su kai dauki.

Wasu hotuna sun nuna wani farin bokiti ya kama da wuta a cikin wani kanti, sai dai a ga girman barnar da fashewar ta yi a tashar jirgin ba.

Rundunar 'yan sanda ta ce "mutane da dama" sun ji rauni sannan ta bayar da shawara ga jama'a su guji zuwa yanki.

Ganau sun ga akalla fasinja daya wanda ya ji rauni a fuska.

Hukumomi sun ce an kai mutum 18 asibiti.

Wasu fasinjojin sun yi matukar kaduwa inda suka fice daga tashar ta Parsons Green.

Hukumar 'yan kwana-kwana ta London ta ce ta aika da ma'aikatanta na gaggawa yankin.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Reuters
Hakkin mallakar hoto Alex Littlefield

Labarai masu alaka