Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon da ya gabata daga 8 - 14 Satumba 2017

Wasu hotuna na musammanda aka zabo na wasu abubuwan da suka faru a fadin nahiyar Afirka.

A man sells socks along a street in Lekki, Lagos, Nigeria September 12, 2017

Asalin hoton, Reuters

A ranar Laraba ne wani mai talla yake zagaya wa da kayansa a jihar Lagos da ke Najeriya.

Asalin hoton, Reuters

A ranar Talata ne wani matafiyi yake kan hanyarsa ta zuwa Kinshasa, da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.

Asalin hoton, Reuters

A ranar Talata ne wannan dalibar ta fito daga makaranta da ke kauyen Michika, a arewa maso gabashin Najeriya.

Asalin hoton, EPA

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya karade wani yankin nahiyar, inda ya yi amfani da nau'o'in sufuri dabam-dabam wajen kai shi bude majalisa a Harare.

Asalin hoton, EPA

Wasu mambobin dakarun Shugaban kasar na jiran isowarsa.

Asalin hoton, AFP

A ranar Juma'a ne dan kwallon Leipzig na kasar Guinea Naby Keita, yake murna bayan da suka yi nasara a lokacin da suka kara a wasan Bundesliga da Hamburger.

Asalin hoton, AFP

A ranar Lahadi ne dan kwallon kungiyar Faransa Guingamp Jordan Ikoko ya yi kokarin kwace kwallo daga wurin Kenny Tete.

A farkon makon da ya gabata ne a Monrovia babban birnin Liberia, magoya bayan jam'iyyar adawa suke yanke shawarar kaddamar da wani gangami na yakin neman zabensu ta hanyar yi wa jikinsu fenti da launin fari da kore.

Asalin hoton, AFP

A ranar Asabar ne yara suka yi dandazo suna kallon wata shiga mai rikitarwa da masu rawar gargajiya na Malawi suka yi, a lokacin da ake wasannin gargajiya na shekara-shekara a Harare.

Asalin hoton, EPA

Wani daga cikin masu gudanar da rawar gargajiyar na takawa a tsakiyar birnin Harare.

Asalin hoton, AFP

A ranar ne dai a wani yankin nahiyar suka shirya domin gabatar da wasannin gargajiya na shekara-shekara da ake yi a Abidjan.