Hotunan rayuwa bayan bala'in zaftarewar kasar Saliyo

Wata daya ya gabata ne, birnin Freetown na kasar Saliyo ya fuskanci bala'in ambaliyar ruwa da zaftarewar laka. Kiyasi ya nuna cewa kusan mutum 800 ne suka mutu, inda a kalla mutum 7,000 kuma suka rasa muhallansu.

Bayan makonni da aka yi ana sheka ruwan sama, tsaunin Sugar Loaf ya rufto ya murkushe gidajen al'ummar da ke zaune a wajen.

Ruwa ya dinga tunkodo laka da duwatsu daga saman tsaunin, inda ya dinga rushe gidaje a wasu yankuna biyu na Kamayama da Kaningo.

Asalin hoton, Olivia Acland

A wata gudan da ya gabata, dubban iyalai ne suka rasa muhallansu suke kuma zaune a sansanin 'yan gudun hijira. A yayin da wasu mutane ke zaune da abokai da 'yan uwansu, sauran kuwa na rabewa ne a ajujuwan makarantu ko gidan dagatai ko kuma a coci.

Fiye da iyalai 200 ne ke zaune a kangwaye kusa da inda zaftarewar lakar ta afku.

A yanzu gwamnatin kasar ta samar da wasu sansanonin biyu a Juba da Hill Station, wadanda hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da hukumomi masu zaman kansu suka samar.

Tuni an fara mayar da wadanda abin ya rutsa da su kuma ba su da wajen zama zuwa sansanonin. Ana gina gidaje masu saukin kudi a yankin Six Mile da ke can wajen birnin Freetown.

Ana tsammanin mutanen da abin ya shafa za su koma can nan da wata uku ko shida masu zuwa.

Duk da cewa an kai taimako da dama kasar kuma mutane da yawa sun samu, wadansu da dama sun ce ba su samu komai ba kuma suna fama da rashin abinci da magani da wurin kwanciya.

Asalin hoton, Olivia Acland

Tun lokacin da zaftarewar laka ya afku, Kadi Kamara da 'yarta mai shekara daya Esme, suke kwana a wani kango da ba abin kwanciya ko abin lulluba.

"Na ji an ce za a mayar da mu daya daga cikin sansanin gwamnati," a cewar Kadi, "amma har yanzu muna nan. Ina zaton sun manta da mu ne. Ba mu ci komai ba tun jiya da safe. Mutane da dama na ta fama da rashin lafiya."

Da aka tambayeta ko an mata rijista don samun taimako daga gwamnati, ko MDD ko sauran hukumomi masu zaman kansu, sai ta ce: "Mun yi rijista da dama da hukumomi daban-daban. Mutane na yin rijista da safe da rana da daddare.

"Na yi rijista da yawa, amma ban sani ba ko daidai na yi. Samun taimakon ma ya zama wahala. Misali, wasu mutanen na samun katifu har uku, amma wasu kamar irinmu ko daya ba mu samu ba."

Asalin hoton, Olivia Acland

Asalin hoton, Olivia Acland

Asalin hoton, Olivia Acland

A daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijirar gwamnati a Juba, wata mata ta damu kan cewa dole ta tafi don ba ta samu katin da ake rabawa ba na shaidar yin rijista.

Asalin hoton, Olivia Acland

"Ina tare da sauran mutane a makaranta a wannan rana, aka ce mana mu je mu karbi abinci. A lokacin da muka dawo Kamayama, sai suka ce an yini ana yi wa mutane rijista don haka mu mun rasa," in ji ta.

Asalin hoton, Olivia Acland

Mariatu Bangura mai shara 12 ta hada kayanta tana jira a mayar da ita sansanin Juba. Ta tsaya a daidai inda da nane gidan iyayenta, ita da Innarta. A ranar da ibtila'in ya faru ta je wajen kakarta, amma dukkan iyayenta sun mutu.

"A yanzu haka ina kula ne da yara bakwai," in ji innarta mai suna Mariah. "Abin na da wahala sosai saboda nima da kyar nake ciyar da iyalina. Na san akwai wadanda abin bai shafe su ba amma suke yin rijista don karbar taimako, amma mu ne ainihin wadanda abin ya shafa kuma mun fi bukatar taimako sosai."

Asalin hoton, Olivia Acland

Esta da Ibrahim Kargbo suna zaune ne a wannan yanki na Kamayama. Suma iyayensu sun mutu.

Esta na gidan wasu 'yan uwansu ne lokacin da abin ya faru, amma Ibrahim na tare da iyayensa a gida.

Ya makale a karkashin wani rufi da ya fado, sai wani makwabcinsu ne ya taimake shi.

A yanzu haka yaran na zama ne da kawunsu, wanda ba shi da hali sosai kuma yana cikin damuwa kan yadda zai kula da su, don haka yana bukatar saya musu littattafai da samar musu kudin abincin tara na makaranta.

Asalin hoton, Olivia Acland

"Yawancin matan sun rasa muhallansu da mazajensu da 'ya'yansu. Wasu daga cikinsu ba su yi nasara ba a tantancewar da aka yi saboda shugabannin yankin sun ce ba su gane su ba. Hakan na nufin ba za su samu taimako ba," in ji Fasto John.

Da aka tambaye shi kan komawa yankin Six Mile, sai ya ce: "In dai har suna da makarantu da coci da masallatai da abubuwan bukatar rayuwa, to ina ga mutane za su yi farin cikin komawa."

Asalin hoton, Olivia Acland

Tuni aka ake ta faman gina gidajen Six Mile.

Mai magana da yawun shugaban kasa Abdulai Baytayray, ya ce: "A bangaren farko na ginin, za mu yi gidaje 53. Za kuma mu gina gidan marayu da asibiti da makaranta.

"Mun ware fili ekta 200 a wannan yankin don yi ginin, don mu samu damar dawo da ba wai wadanda bala'in zaftarewar lakar ya shafa ba kawai, har ma da duk wadanda ke zaune a yankuna masu hadari a birnin Freetown."

Asalin hoton, Olivia Acland

Dukkan hotunan an samo su ne daga Olivia Acland.